Abin da ke Faruwa tsakanin Iyalan Marigayi Albani Zariya da Cibiyar Darul Hadith

Abin da ke Faruwa tsakanin Iyalan Marigayi Albani Zariya da Cibiyar Darul Hadith

  • Cibiyar Darul Hadis da ke Zariya ta yi karin haske kan batun neman taimako da ake yi wa ‘yar marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani
  • Dan marigayi Albani, Abdulrahman Muhammad Adam, ya yi dogon bayani kan alakar makarantar da mahaifinsu ya bari da kuma rayuwarsu
  • Abdulrahman Muhammad Adam ya yi bayani kan yadda aka raba musu gado da kuma yadda rayuwa ta kasance a gare su bayan kashe mahaifinsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - An samu karin bayanai bayan barkewar wani rahoto da ke cewa ’yar marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya ba ta da lafiya kuma ana nema mata taimako.

Bayan yaduwar labarin, Cibiyar Darul Hadis da Sheikh Albani Zariya ya assasa ta fito fili domin bayyana abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kama 'yan 'daɗi soyayya' da suka yi aure a wurin shakatawa a Kano

Sheikh Albani
Dan Albani ya yi magana kan alakarsu da Darul Hadis. Hoto: Albaniy TV
Asali: Facebook

A wata hira da tashar Albani TV ta yi da babban dan marigayin, Abdulrahman Muhammad Adam, ya musanta zargin cewa ba a taimakawa ’ya’yan malamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdulrahman Muhammad Adam ya ce makarantar da mahaifinsu ya bari na daukar nauyinsu tun bayan da aka kashe Sheikh Albani Zariya.

Bayani kan rashin lafiyar ’yar Albani

Abdulrahman ya ce bai da wata masaniya kan batun neman taimako ga wata kanwarsa da ba ta da lafiya sai da mijinta, Malam Sani Ladan, ya kirashi ya shaida masa cewa an turo masa kudi.

Ya ce Malam Sani Ladan ya ce masa wani malami mai suna Bello Yabo ya turo masa taimakon N100,000 a kan rashin lafiyar matarsa.

Abdulrahman ya bayyana cewa da ya tuntubi kanwarsa, ta tabbatar masa cewa ita ba ta nemi a taimaka mata da kudi ba, sai dai ta taba yin hira mai kama da haka da kawarta.

Kara karanta wannan

'Qur'anic Festival': Bala Lau ya yi raddi ga Sheikh Jingir, ya tuno rashin mutunci da ya yi masa

A kan rashin lafiya kuma, ya ce likitoci sun tabbatar mata cewa tana fama da matsalar koda, amma ana sa ran za ta samu sauki bayan haihuwarta.

Bugu da kari, Abdulrahman ya ce kanwarsa ta taba zuwa wajen daraktan makarantar domin neman kudi saboda kula da lafiyarta, inda aka ba ta N60,000.

'Ya'yan Albani za su karbi makarantarsa?

Abdulrahman ya ce akwai wasu da suka nuna sha’awar kwace makarantar da Sheikh Albani ya yi wakafi da ita a cikinsu.

Ya ce kannensa sun zo gare shi da batun, amma ya ki amincewa ya nuna musu mahaifinsu ya riga ya yi wakafi da ita.

Ya kara da cewa bayan rasuwar mahaifinsu, an raba gadonsa, ciki har da motarsa kirar Toyota Camry wacce aka ba shi.

Baya ga haka, ya bayyana cewa mijin wata kanwarsa yana daga cikin wadanda ke goyon bayan a karbe makarantar. Ya ce har ana shirin kai batun kotu domin neman mallakarta.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Darul Hadith na daukar nauyin 'ya'yan Albani?

Abdulrahman ya ce Cibiyar Darul Hadis na daukar nauyin ’ya’yan marigayin tun bayan rasuwarsa.

Ya ce makarantar na ba su abinci, kudin makaranta da kuma tallafin kudin kashewa ga wadanda suke karatu a makarantu.

Sannan ya kara da cewa duk lokacin da dalibi zai tafi makaranta, ana tura masa kudin abinci da na kashewa.

Haka zalika, a lokacin bukukuwan Sallah, Abdulrahman ya bayyana cewa ana musu hidima kamar haka:

  • Raguna biyu (A lokacin babbar sallah)
  • Kudin cefane
  • Kaji (A lokacin karamar sallah)
  • Tufafin sallah

Batun gidan marigayi Sheikh Albani

Dangane da gidan marigayin, Abdulrahman ya ce asali yana cikin gado, amma saboda sabani, sai makaranta ta saye shi.

Daga nan aka raba kudin ga ’yan uwasa a matsayin gadonsu sannan aka ba kowa damar ci gaba da zama a cikinsa.

Kara karanta wannan

Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron

Ya bayyana cewa tsohon daraktan makarantar, Farfesa Abdulra’uf, ne ya kawo shawarar sayen gidan, inda aka saye shi da kudin da ya kai Naira miliyan 20 zuwa 30.

Abdulrahman ya ce a halin yanzu, akwai ’ya’yan marigayin biyu da suka yi aure suna zaune a gidan.

Wanene ya mallakai cibiyar Darul Hadith?

Abdulrahman ya bayyana cewa makarantar da Cibiyar Darul Hadis ba mallakar wani mutum daya ba ne ko wasu cikin 'ya'yansa, illa mallakar al’ummar Musulmi.

Ya ce duk wanda yake son karatu ko koyarwa, makarantar ta ba da damar haka kasancewar mahaifinsu ya yi wakafi da ita.

Haka kuma, ya bayyana cewa yana aiki a makarantar, haka zalika kaninsa ma yana aiki a makarantar.

Kungiyar Izala ta taimaki 'ya'yan Albani

Abdulrahman ya kuma bayyana cewa kungiyar Izala ta taba turo musu taimakon N500,000, wanda aka raba ga dukkan ’ya’yan marigayin, ciki har da wadanda suka yi aure.

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Sai dai duk da bayanin da ya yi, wasu daga cikin 'ya'yan marigayin sun nuna shakku a kan abin da ya fada inda suka bukaci su ma a yi hira da su a tashar Albani TV.

Yadda ake rikici a masallacin Sahaba a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala ta yi magana kan rikicin masallacin da ake a jihar Kano da Sheikh Muhammad Bin Usman.

Sheikh Muhammad Bin Usman ya bayyana a wata huduba da ya yi cewa an zalunce shi a masallacin Sahaba na Kano amma Izala ta ce ba a zalunce shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng