Tsohon Shugaban NHIS Ya Gamu da Cikas a gaban Kotu bayan EFCC Ta Cafke Shi

Tsohon Shugaban NHIS Ya Gamu da Cikas a gaban Kotu bayan EFCC Ta Cafke Shi

  • Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Usman Yusuf zai ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC
  • Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja, ta ƙi amincewa da buƙatar neman belin da tsohon shugaban na hukumar NHIS ya gabatar
  • Alƙalin kotun ya ƙi amincewa da buƙatar belin ne saboda hukumar EFCC na son yin gyare-gyarenlna tuhume-tuhumen da take yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kuje cikin birnin Abuja, ta yi hukunci kan buƙatar beli da tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Usman Yusuf, ya nema.

Babbar kotun ta yi watsi da buƙatar belin da Farfesa Usman Yusuf ya gabatar a gabanta a yayin zamanta na ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

Kotu ta ki ba da belin Usman Yusuf
Kotu ta hana belin Usman Yusuf Hoto: @Akinyede
Asali: Twitter

EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban NHIS

Jaridar The Cable ta rahoto cewa hukumar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Usman Yusuf a gaban kotun bisa zargin aikata zamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an hukumar EFCC sun kama tsohon shugaban na hukumar NHIS ne a gidansa a ranar Laraba.

Wace tuhuma ake yi wa Farfesa Usman Yusuf?

A cewar takardun kotu, EFCC ta zargi Usman Yusuf da yin amfani da matsayinsa a wancan lokacin, wajen sayen wata mota a kan kudi Naira miliyan 49.197,750, saɓanin Naira miliyan 30 da aka ware a kasafin kuɗi.

Hukumar EFCC ta kuma zargi Usman Yusuf da alaƙa da wani kamfani mai suna GK Kanki Foundation, tare da bayar da kwangilar Naira miliyan 10.1 ba tare da bin ka'ida ba, domin horar da mutane 90, alhali a zahiri mutane 45 ne kawai aka horar.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban NHIS, Usman Yusuf ya shiga matsala, EFCC ta kutsa gidansa a Abuja

Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar beli

A zaman kotun na ranar Alhamis, alƙalin kotun, Chinyere Nwecheonwu, ya ɗage gurfanar da Usman Yusuf domin ba hukumar yaƙi da cin hancin damar gyara tuhume-tuhumen da take masa.

Lauyan wanda ake ƙara mai suna Isah Dokto Haruna, wanda ya wakilci O.I. Habeeb, ya gabatar da buƙatar neman belin Usman Yusuf.

Sai dai alƙalin ya ƙi amincewa da buƙatar belin, bisa dalilin cewa an ɗage zaman gurfanar da wanda ake ƙarar.

Kotun ta ba da umarnin a ci gaba da tsare Usman Yusuf a hannun hukumar EFCC, rahoton Daily Nigerian ya tabbatar.

Alƙalin kotun ya kuma ɗage zaman gurfanar da tsohon shugaban na hukumar NHIS zuwa ranar 3 ga watan Fabrairun 2025.

Sheikh Gumi ya magantu kan cafke Usman Yusuf

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanannen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana kan kamun da hukumar EFCC ta yi wa Farfesa Usman Yusuf.

Kara karanta wannan

"An mari babban jigo," Jami'an tsaro sun mamaye hedkwatar PDP ta ƙasa a Abuja

Sheikh Gumi ya gargaɗi shugaban ƙasa Bola Tinubu kan cewa bai dace jami'an tsaro su riƙa farautar mutanen da suke sukar gwamnatinsa ba.

Malamin addinin musuluncin ya yi zargin cewa kamun da aka yi wa tsohon shugaban na hukumar NHIS akwai alamun ramuwar gayya a ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel