Matar Tinubu Ta ba da Mamaki a Kwara, Ta Fita a Mota Ta Tattauna da Dalibai

Matar Tinubu Ta ba da Mamaki a Kwara, Ta Fita a Mota Ta Tattauna da Dalibai

  • Uwargidan Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, ta dakatar da jerin gwanon motocinta a Kwara don gaisawa da daliban makaranta
  • An ruwaito cewa Sanata Oluremi Tinubu ta bukaci daliban da su dage da karatu domin kyautata rayuwarsa yayin da suka gaisa
  • Matar shugaban kasar ta kai ziyara Kwara ne domin kaddamar da ayyuka da gwamnan jihar ya yi ciki har da wasu manyan gadojin sama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta janyo hankalin jama’a yayin da ta dakatar da jerin gwanon motocinta domin gaisawa da daliban makaranta a Jihar Kwara.

Wannan abu ya faru ne a yayin ziyarar aikinta zuwa jihar, inda daliban suka fito daga makarantu suna ta murna da yi mata maraba.

Kara karanta wannan

Abincin wasu ya kare: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 5, an maye gurbinsu nan take

Matar Tinubu
Matar shugaban kasa ta gaisa da 'yan makaranta a Kwara. Hoto: @KukoyiBusola
Asali: Twitter

Hadimar Remi Tinubu, Busola Kukoyi ta wallafa a X cewa lamarin ya ja hankalin al'umma kuma mutane da dama sun yaba wa matar shugaban kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasancewar ta ji dadin ganain 'ya makarantar, Sanata Remi Tinubu ta ba su shawarwari masu muhimmanci, musamman a kan karatu.

Yayin ziyarar, matar shugaban kasar ta aza tubalin asibiti da aka sanya wa sunanta da zai bunkasa harkar kiwon lafiya a jihar.

Oluremi Tinubu ta gaisa da dalibai

A wani abin da ya ba da mamaki a jihar Kwara, matar shugaban kasa ta dakatar da rukunin motocinta domin gaisawa da 'yan makaranta.

Jaridar Punch ta wallafa cewa daliban sun fito daga makaranta ne domin yi wa Uwargidan Shugaban Kasar maraba yayin da take wucewa.

Sai dai maimakon ta wuce, sai ta tsaya, ta fita daga motarta, tana gaisawa da su tare da ba su shawari kan rayuwa.

Kukoyi ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin Kano ta fusata bayan gano abin da ake yi a gidajen da Kwankwaso ya gina

"Lokacin da ta hango yaran suna shewa da murna, sai ta ce a bar batun tsaro a gefe, ta sauka daga mota domin gaisawa da su."

A yayin tattaunawarta da daliban, ta bukaci su dage da karatu tare da guje wa duk wani hali da zai iya hana su cimma burinsu.

Wannan matakin nata ya burge jama’a da dama, inda mutane suka yaba da irin saukin kai da kulawarta ga 'yan kasa

Remi Tinubu ta kaddamar da ayyuka

Oluremi Tinubu ta kaddamar da rabon kayayyaki ga mata a karkashin shirin Renewed Hope Initiative.

A karkashin shirin, an raba kayayyaki da nufin tallafa wa wajen bunkasa harkar lafiya, musamman wajen kula da mata masu juna biyu da jarirai.

Bugu da kari, ta bude manyan gadoji guda biyu a Ilorin, wadanda suka hada da:

  • Gadar Janar Babatunde Idiagbon
  • Gadar Dr Ibrahim Sulu-Gambari

Wadannan gadoji na daga cikin manyan ayyukan da ake aiwatarwa domin rage cunkoson ababen hawa da kuma habaka ci gaban tattalin arziki a jihar

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Haka zalika, uwargidan shugaban kasar ta aza tubalin sabon asibiti mai suna Asibitin Oluremi Tinubu a Ilorin.

Gwamnatin Kwara ta bayyana cewa ana fatan asibitin zai taimaka wajen inganta harkar kiwon lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

Mutane sun yabi Oluremi Tinubu

Bayan bayyanar labarin, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan yadda Uwargidan Shugaban Kasar ta nuna kulawa ga dalibai 'yan makaranta.

Wasu sun bayyana hakan a matsayin misali na shugabanci na gari, yayin da wasu ke ganin hakan wata hanya ce ta kusantar da gwamnati ga al’umma.

An gina titin Tafawa Balewa a Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kwara ta sanya wa wani katafaren titi sunan Alhaji Abubakar Tafawa Balewa.

Legit ta wallafa cewa gwamnan Kwara ya ce Alhaji Abubakar Tafawa Balewa ya bayar da gudunmawa sosai wajen gina Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel