Ana Fama da 'Yan Bindiga, Gwamna Ya Bankado Wata Barazana ga Tsaro
- Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya kai ziyayar jaje a ƙauyen da aka wani abin fashewa ya tarwatse a gidan wani mai haƙar ma'adanai
- Umaru Bago ya koka kan yadda wasu masu haƙar ma'adanai suke da bindigogi da ababen fashewa, inda ya ce hakan barazana ce ga tsaro
- Gwamnan Neja ya kuma yi kira ga masu ababen fashewa da su miƙa su ga hukumomim da suka dace maimakon su ajiye su a cikin gida
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana cewa masu haƙar ma'adanai na haifar da barazana ga tsaro.
Gwamna Bago ya bayyana cewa wasu masu haƙar ma'adanai a sassan jihar suna da bindigogi da abubuwan fashewa, wanda hakan babbar barazana ce ga tsaro.

Asali: Twitter
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyararsa zuwa ƙauyen Sabon-Pegi da ke ƙaramar hukumar Mashegu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bago ya kai ziyarar jaje
Gwamna Bago ya je ƙauyen ne sakamakon fashewar wata nakiya a gidan wani mai haƙar ma'adanai, wacce ta yi sanadiyyar hallaka mutum uku tare da jikkata wasu da dama.
Ya bayyana cewa jihar Neja na da arziƙin zinare da lithium, wanda ke janyo hankalin masu haƙar ma’adanai daga sassa daban-daban.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda wasu daga cikin waɗannan masu haƙar ma’adanan suke ɓoye abubuwan fashewa da makamai, abin da ke ƙara matsalar taɓarɓarewar rashin tsaro a yankin.
"Muna kira ga jama’a da su miƙa waɗannan makamai da abubuwan fashewa ga kwamitin tsaro da ya ƙunshi jami’an tsaro, hukumonin NEMA, NSEMA, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki."
"Domin ajiyarsu a wurin da ya dace maimakon a riƙa ajiye su a cikin gida."
- Gwamna Umaru Bago
Gwamnan ya kuma bada tallafin naira miliyan 174 domin tallafawa mutanen da fashewar ta shafa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2
Minista ya wakilci Tinubu a Neja
A yayin ziyarar, gwamnan yana tare da ministan watsa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, Sanata Abubakar Sani Bello da wasu manyan jami’an gwamnati.
Mohammed Idris ya miƙa saƙon ta’aziyyar shugaban ƙasa dangane da lamarin, yana mai cewa wannan musiba ce da za a iya kauce mata.
"Shugaban ƙasa ya umarci hukumar kula da wayar da kan jama’a (NOA) da ta ƙara faɗakar da jama’a, musamman masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, domin kaucewa faruwar irin wannan hatsarin a nan gaba."
- Mohammed Idris
Haka nan, shugaban ƙasa ya umarci ma’aikatar harkokin jin ƙai, hukumar NEMA da sauran hukumomin tarayya da su tallafawa gwamnatin jihar Neja wajen bayar da agaji ga al’ummar da abin ya shafa.
Sojoji sun ragargaji ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai, sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Sojojin sun yi ruwan bama-bamai kan ƴan ta'addan na Boko Haram, inda suka samu nasarar hallaka da yawa daga cikinsu tare da raunata wasu da dama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng