'Ban Son Belin': Sowore Ya Buga da 'Yan Sanda, Ya Ce Ya Fi Tinubu Karfin Iko a Baya

'Ban Son Belin': Sowore Ya Buga da 'Yan Sanda, Ya Ce Ya Fi Tinubu Karfin Iko a Baya

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya ce ba zai yarda Shugaba Bola Tinubu ya tsaya masa a harkar beli ba
  • Ana tsare da Omoyele Sowore a hannun ‘yan sanda bayan da aka tuhume shi da cin zarafin wasu jami’an tsaro ta yanar gizo
  • Bayan gurfanar da shi a kotu, ya ƙi amincewa da sharuɗan beli da suka haɗa da mika fasfo dinsa da samar da babban ma’aikacin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dan takarar jam’iyyar AAC a zaɓen 2023, Omoyele Sowore ya bayyana cewa ba zai karɓi shugaba Bola Tinubu a matsayin mai taimaka masa a karbar beli ba.

An kama Sowore ne bayan ce-ce-ku-ce da ‘yan sanda a Lagos kuma ya ce sharuɗan da aka gindaya masa domin samun beli abin dariya ne kuma cin mutunci ne a gare shi.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna ya tono abin da ƴan Najeriya ba su sani ba game da Bola Tinubu

Sowore
Sowore ya kalubalanci sharudan belin da aka ba shi. Hoto: Bayo Onanuga|Omoyele Sowore
Asali: Twitter

The Cable ta rahoto cewa Sowore ya yi bayani ne yayin hira da 'yan jarida bayan 'yan sanda sun yi maganar belinsa a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin tsare Yele Sowore a Abuja

‘Yan sanda sun kama Sowore ne bisa zargin cin zarafi ta yanar gizo da wasu ayyukan da suka shafi barazana.

Wannan ya biyo bayan wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, inda aka nuna Sowore yana inkari wa ‘yan sanda kan ikon tsaida motarsa a wani shingen bincike a Lagos.

A ranar Litinin Sowore ya amsa kiran ‘yan sanda a hedkwatar su da ke Abuja, kuma daga baya aka gurfanar da shi a kotu a ranar Laraba bisa zargin aikata laifuffukan sadarwa ta yanar gizo.

Sowore ya ki yarda da sharuɗɗan beli

Bayan gurfanar da shi a kotu, ‘yan sanda sun gindaya masa wasu sharuɗɗa kafin su bayar da belinsa.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

Daga cikin sharuɗɗan akwai cewa dole ne ya mika fasfo dinsa, sannan kuma ya samo wani babban ma’aikacin gwamnati mai matsayi na 17 domin tsaya masa.

Sahara Reporters ta wallafa cewa Sowore ya ce ba zai amince da wadannan sharuɗan ba yana mai cewa:

"Ba zan yarda da waɗannan sharudɗan ba domin sun sabawa doka kuma ba su da tushe.
"Wane dalili ne da zai sa a ce dole ne wani babban ma’aikaci mai matsayi na 17, wanda ake naɗawa ne ta fuskar siyasa, ya tsaya min?"

Ya kuma ƙara da cewa:

"Na yi gwagwarmayar kawar da cin hanci da rashawa, kuma yanzu ana neman in nemo wani wanda ke da kadarar N100m domin ya tsaya mani.
"Wannan dai ba abu ne mai yiwuwa ba!"

'Ko Tinubu zai tsaya mani, zan ki' - Sowore

Sowore ya bayyana cewa tun shekarar 1992 yana fafutukar kare dimokuraɗiyya a Najeriya, lokacin da Tinubu ke matsayin Sanata.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

A cewarsa:

"A 1992, lokacin da nake shugabancin dalibai, Tinubu Sanata ne amma ni na fi shi ikon fada a ji a Najeriya."

Ya kuma ƙalubalanci sufeton ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, yana mai cewa shi dan kundunbala ne:

"A wancan lokacin, Egbetokun yana yiwuwa sabon ɗan sanda ne da bai wuce matsayin Sajan ba. Hakan ma idan bai yi karyar shekaru ba kenan!"

An kama mai safarar makamai a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an DSS sun kama wani matashi da ake zargi da safarar makamai daga Nijar zuwa Najeriya.

Shugaban DSS na jihar Zamfara ya gabatar da wanda aka kama din ga gwamnan jihar, Dauda Lawal a fadar gwamnati da ke Gusau.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel