Tsohon Shugaban NHIS, Usman Yusuf Ya Shiga Matsala, EFCC Ta Kutsa Gidansa a Abuja

Tsohon Shugaban NHIS, Usman Yusuf Ya Shiga Matsala, EFCC Ta Kutsa Gidansa a Abuja

  • Tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf ya shiga hannun jami'an EFCC a gidansa da ke Abuja
  • Dakarun EFCC sun kai samame gidansa ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, 2025 kuma sun kama shi, za a gurfanar da shi a gaban kotu
  • Tun a zamanin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari aka shigar da ƙorafi kansa wanda daga karshe aka kire shi daga matsayinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa watau EFCC ta cafke tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.

Jami'an EFCC sun cafke tsohon shugaban NHIS ne yayin da suka kai samame gidansa da ke birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

Yusuf Usman.
Jami'an EFCC sun kama Farfesa Usman Yusuf, tsohon shugaban NHIS a Abuja Hoto: @Akinyede
Asali: Twitter

EFCC ta kama tsohon shugaban hukumar NHIS

Mai magana da yawun hukumar EFCC na ƙasa, Dele Oyewale ya tabbatar da kamen a wata hira da ya yi da Channels tv.

Kara karanta wannan

Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyewale ya tabbatar da cewa jami’an hukumar EFCC sun kai samame gidan Farfesa Usman Yusuf kafin daga bisani su kama shi.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu ranar Alhamis, 30 ga Janairu, 2025, don fuskantar tuhuma.

Meyasa aka kama Farfesa Usman Yusuf?

Bincike ya nuna cewa an shigar da korafi a kansa tun a zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta hannun ma’aikatar lafiya ta tarayya.

Ana zargin tsohon shugaban NHIS da aikata ba daidai ba da kuma wasu ayyukan damfara.

A shekarar 2019, aka tsige Usman Yusuf daga mukaminsa bayan wani kwamitin bincike da Ma’aikatar Lafiya ta kafa ya ba da shawarar a kore shi.

Ana zarginsa da karkatar da N919m

Kwamitin ya zarge shi da almundahanar Naira miliyan 919, lamarin da ya sa gwamnatin Buhari ta amince da dakatar da shi daga aiki.

Farfesa Usman Yusuf ya shahara wajen sukar manufofin gwamnati, musamman a fannin kiwon lafiya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban NHIS: Gumi ya zargi Tinubu da kama 'yan adawa da manufar siyasa

Tun da aka sauke shi daga mukaminsa, ya rika sukar yadda ake tafiyar da harkokin NHIS da kuma batun yaki da cin hanci a Najeriya.

Yanzu dai ana jiran ganin irin tuhumar da EFCC za ta gabatar a kansa a gaban kotu, yayin da al’ummar kasa ke ci gaba da bibiyar lamarin don ganin ko zai fuskanci hukunci.

Yahaya Bello: EFCC ta fara gabatar da shaidu

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta fara gabatar da shaidu a shari'ar tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello.

Sai dai bayan sauraron shaida ɗaya tal, babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ɗage zaman shari'ar zuwa watan Afrilu da Mayun 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel