NLC da Wasu Manyan Ƙungiyoyi da Suka Nunawa Gwamnati Yatsa kan Karin Kuɗin Kira

NLC da Wasu Manyan Ƙungiyoyi da Suka Nunawa Gwamnati Yatsa kan Karin Kuɗin Kira

Batun ƙarin kudin kiran waya, sayen data da tura sako a Najeriya na ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da ake surutu a kansu kwanan nan.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Idan ba ku sha'afa ba, gwamnatin tarayya ta amince kamfanonin sadarwa su ƙara kaso 50% a kuɗin kiran waya da sauran harkokin sadarwa.

Bola Tinubu.
Yadda aka fa yi wa Gwamnatin Tinubu ca kan karin kuɗin kira a Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta amince da ƙarin kudin waya

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta ƙasa (NCC) ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NCC ta amince da ƙarin ne bayan kamfanonin sadarwa da suka haɗa da MTN, Airtel, Glo da sauran makamantansu sun nemi kara kuɗin da kaso 100%.

Amma gwamnatin tarayya ta ce hakan ba zai yiwu ba domin wahalar za ta yi wa ƴan Najeriya yawa, ta amince dai a yi ƙarin kaso 50%.

Kara karanta wannan

NLC ta fadi wuraren taruwa a jihohi da lokacin zanga zangar karin kudin kira

Sai dai wannan mataki wanda ya fito daga hukumar NCC bai yi wa galibin ƴan Najeriya daɗi ba, a cewarsu wannan ƙarin wahala ce kan wahala.

Manyan kungiyoyin da suka yi watsi da ƙarin

Hakan ya a manyan kungiyoyin fararen hula suka fito suka nuna ɓacin ransu da wannan ƙari, wanda suke ganin bai zo a lokacin da ya dace ba.

A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro maku jerin waɗannan ƙungiyoyi da suka fito ƙarara suka ƙi aminta da ƙarin kuɗin kira a Najeriya, ga su kamar haka:

1. Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC)

Ƙungiyar kwadago watau NLC na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi na sahun gaba da suka yi fatali da ƙarin kiɗin kira, sayen data da tura saƙo a Najeriya.

NLC ta soki ƙarin kuɗin sadarwa, tana mai cewa hakan zai karawa ƴan ƙasa da ma'aikata wahala a daidai lokacin da suke fama da matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

NLC: Karin kudin kiran waya ya sake tayar da ƙura, an shirya gagarumar zanga zanga

A wata sanarwa da ta wallafa a shafin X, shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce gwamnatin tarayya ta yi kuskure da ta amince da karin kudin waya a wannan lokacin.

Ajaero ya ce ƙaramin ma'aikaci mai samun N70,000 a wata, yana kashe kaso 10% (N7,000) a sadarwa, idan aka yi ƙarin kudin za su ƙaru zuwa N10,500.

"Mai samun mafi karancin albashi na N70,000 a wata yana kashe kusan 10% a kan sadarwa. Wannan karin zai kusan ninka abin da yake kashewa daga N7,000 zuwa N10,500 a wata.
"Idan ku ka duba hakan ya kai kusan 15% na albashinsa, wannan tsadar ba za a iya jurewa ba," in ji Ajaero.

NLC ta yanke shawarar fita kan tituna zanga-zangar adawa da ƙarin kuɗin kira a faɗin ƙasar nan ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu, 2025.

2. Gamayyar ƙungiyoyin Arewa (CNG)

Haka nan kuma gamayyar ƙungiyoyin Arewa watau CNG ta nuna damuwa da ƙarin kudin kiran da gwamnatin tarayya ta amince da shi a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

CNG ta bayyana karin kudin sadarwa a matsayin cin zarafi ga ‘yan Najeriya, musamman ganin yadda tattalin arziki ke ƙara tabarbarewa.

Shugaban ƙungiyar, Jamilu Aliyu Charanchi, ya ce wannan mataki ba daidai ba ne, kuma ba zai amfanar da komai ba face ƙara wa mutane raɗaɗi.

CNG ta bukaci ‘yan Najeriya da ƙungiyoyin farar hula su haɗu wuri guda da murya ɗaya, su yi fito-na-fito da karin, sannan su nemi a janye shi.

3. Kungiyar SERAP ta kai ƙara kotu

Kungiyar SERAP mai gwagwarmayar kare hakkokin tattalin arziki ta yi watsi da ƙarin kudin kiran da aka yi a ƙasar nan.

SERAP ta bayyana ƙarin kuɗin kira da kaso 50% a matsayin wanda aka yi ba bisa ƙa’ida ba, kuma ya saɓawa doka.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, SERAP ta bayyana cewa ta maka gwamnatin tarayya a gaban kotu, inda ta buƙaci a dakatar da aiwatar da karin kudin sadarwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

A ƙarar da ta shigar mai lamba, FHC/ABJ/CS/111/2025 a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP ta yi iƙirarin cewa ƙarin kudin ya keta haƙƙin ƴan ƙasa.

"SERAP na neman kotu ta hana gwamnatin Tinubu da kamfanonin sadarwa aiwatar da ƙarin kuɗin sadarwa na kashi 50%," in ji sanarwar.

3. Kungiyar Take It Back Movement

Wannan ƙungiyar ta kare hakkin bil’adama ta soki matakin NCC na amincewa da karin kudin kira, tana mai cewa hakan zai ƙara wa mutane wahala.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da NCC da su soke karin nan take, ko kuma su fuskanci zanga-zanga a fadin ƙasar.

Waɗannan ƙungiyoyi na ƙorafi cewa bai dace a yi karin kuɗin sadarwa ba musamman ganin wahalhalun tattalin arziki da mutane ke fuskanta.

Shehu Sani ya nemi a janye karin kudin kira

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa Majalisar tarayya na da ikom hana aiwatar da ƙarin kudin kira da NCC ta yi.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya ce yana fatan shugabannin Majalisun Tarayya biyu za su yi amfani da wannan iko su hana kamfanoni ƙarin kudin kira a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262