Gwamnan Bauchi Ya Kasa Hakura, Ya Yi Wa Ministan Tinubu Martani Mai Zafi
- Gwamnatin jihar Bauchi ba ta ji daɗin sukar da ministan harkokin ƙasashen wajje, Yusuf Tuggar, ya yi wa Gwamna Bala Mohammed ba
- Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Bauchi ya zargi ministan da gazawa a muƙamin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi
- Aminu Hassan Gamawa ya bayyana cewa ministan bai san abubuwan da ke faruwa ba a jihar saboda yawace-yawacen da yake yi a ƙasashen waje
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta yi martani mai zafi ga ministan harkokin ƙasashen waje a gwamnatin Bola Tinubu, Yusuf Tuggar.
Martanin na zuwa ne bayan ministan ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed kan sukar da yake yi wa ƙudirin haraji.

Source: Twitter
Martanin na cikin wata sanarwa ne da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Bauchi, Aminu Hassan Gamawa, ya fitar a madadin gwamnan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bauchi ta caccaki Yusuf Tuggar
Dr. Aminu Hassan Gamawa ya bayyana Yusuf Tuggar a matsayin mara ƙwarewa a diflomasiyya mai neman damar siyasa don moriyar kansa, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Gamawa ya zargi Yusuf Tuggar da rashin kallon gazawarsa a muƙamin da aka ba shi, amma ya maida hankali wajen sukar gwamnan Bauchi.
Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin ya bayyana cewa ministan ya gaza a aikinsa amma ya fi mayar da hankali kan sukar Gwamnan Bauchi, wanda manufofinsa a ɓangaren noma suka jawo tagomashi ga jihar Bauchi.
"Abin mamaki ne cewa Tuggar, wanda ɗan asalin Bauchi ne, bai san waɗannan abubuwan ba. Idan da yana zama a jiharsa maimakon yawan yawace-yawace a ƙasashen waje, da ya fahimci irin sauyin da Bala Mohammed ya kawowa Bauchi."
"Rashin kusancinsa da talakawa da kuma yankinsa, wanda har shugaba Bola Tinubu bai iya cin zaɓe a can ba, yana nuna rashin tasirinsa a wurin mutanen da yake iƙirarin wakilta."
Ministan Tinubu ya jawowa Najeriya abin kunya
Har ila yau, shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin ya zargi Tuggar da gazawa wajen jagorantar ECOWAS, wacce a baya ƙungiya ce mai ƙarfi da haɗin kai, amma yanzu tana fuskantar rikice-rikice.
"Gurguwar shawararsa ga shugaba Tinubu kan rikice-rikicen yankin Sahel ya haifar da ficewar ƙasashe masu muhimmanci kamar Mali, Burkina Faso, da Nijar daga ƙungiyar."
"Wannan gagarumar gazawa ce da ba a taɓa yin irinta ba a tarihin jagorancin Najeriya a yankin Afirika ta Yamma."
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnaatin ya bayyana cewa zargin da Tuggar ya yi wa Bala Mohammed dangane da amfani da filaye a Bauchi ƙarya ce kawai don ɓata suna.
Dogara ya faɗi yadda aka taimaki gwamnan Bauchi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana aka taimaki gwamnan Bauchi, ya samu tikitin takarar PDP a zaɓen 2019.
Yakubu Dogara ya bayyana cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi wa Bala Mohammed riga da wanda a lokacin amma yanzu ya koma yana yi masa butulci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

