Yaki Ta Talauci: Gwamnan Jigawa Ya Raba Tallafin Kudi ta Katin ATM
- Rahotanni sun nuna cewa mutane 23,000 za su amfana da shirin rabon katin ATM a jihar Jigawa domin rage musu radadin rayuwa
- Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya yi kira da a yi adalci da gaskiya wajen rabon katin ga mutanen da za su amfana da shirin
- Haka zalika gwamnatin jihar Jigawa ta gargadi masu cin gajiyar shirin kan amfani da kuɗin da za su samu ta hanyoyin da suka dace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya kaddamar da rabon katin cirar kuɗi (ATM) ga mabuƙata ƙarƙashin shirin tallafin gwamnatin tarayya (NSIP).
Wannan ne zagaye na biyu na shirin kuma mutane 23,000 ne za su amfana da kuɗin tallafin da aka ware domin rage radadin talauci a jihar.

Kara karanta wannan
Abincin wasu ya kare: Gwamna ya fatattaki kwamishinoni 5, an maye gurbinsu nan take

Asali: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook cewa an gudanar da taron ne a ranar Laraba, 29 ga Janairu, 2025, a sakatariyar ƙaramar hukumar Dutse.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Namadi ya yabawa gwamnatin tarayya bisa kawo shiri da ke da nufin tallafa wa al’umma, yana mai cewa yana da nasaba da manufofin gwamnatinsa na rage fatara.
Gwamna Namadi ya bukaci a yi adalci
A jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da shirin, Gwamna Namadi ya yi kira ga jami’an da ke kula da rabon katin da su gudanar da aikin cikin gaskiya da adalci.
Gwamnan ya ce:
"Shirin na da matuƙar muhimmanci, kuma wajibi ne a tabbatar da cewa an aiwatar da shi bisa gaskiya da rikon amana domin amfanin waɗanda suka cancanta."
Haka nan, gwamnan ya bukaci masu cin gajiyar shirin, musamman mata, da su yi amfani da kuɗin ta hanyoyin da za su amfanar da su da iyalansu.
Gwamna Umar Namadi ya shawarce su da su saka jari ko yin sana’o’i da kudin domin samun ci gaba mai dorewa.
Faɗaɗa shirin tallafin gwamnati a Jigawa
A yayin taron, Gwamna Namadi ya bayyana cewa gwamnatin jihar Jigawa ta faɗaɗa wasu tsare-tsaren tallafi domin amfanin al’umma, kamar haka;
- An ƙara faɗaɗa shirin ciyar da ɗalibai a makarantun firamare daga aji 1-3 zuwa aji 4-6
- Gwamnatin jihar ta ɗauki ma’aikata sama da 6,000 a fannonin ilimi, lafiya da noma ƙarƙashin shirye-shiryen J-TEACH, J-HEALTH, da J-AGRO
- Ana cigaba da shirye-shiryen tallafawa ƙananan yara da mata masu juna biyu domin inganta rayuwarsu
Gwamnan ya jaddada cewa waɗannan matakai na daga cikin muradun gwamnatinsa guda 12 da suka mayar da hankali kan jin daɗin al’umma da rage fatara.
Gwamna Namadi ya yabi gwamnatin tarayya
Daga ƙarshe, Gwamna Namadi ya gode wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayan da yake bai wa Jihar Jigawa a shirye-shiryen jin daɗin al’umma.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan
Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da rabon katin ATM a sauran ƙananan hukumomin jihar domin tabbatar da cewa duk waɗanda suka cancanta sun amfana da shirin.
Ya kuma gargadi jami’an da ke kula da rabon kuɗin da su guji nuna son rai ko yin almundahana, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Ramadan: Za a ciyar da mabukata a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa ya ware biliyoyi domin ciyar da mabukata a watan azumin Ramadan na 2025.
Legit ta rahoto cewa mabukata 189,000 ne za su amfana da shirin kamar yadda kwamishinan yada labaran jihar, Hon. Sagir Musa ya tabbatar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng