NLC: Karin Kudin Kiran Waya da Ya Sake Tayar da Ƙura, An Shirya Gagarumar Zanga Zanga

NLC: Karin Kudin Kiran Waya da Ya Sake Tayar da Ƙura, An Shirya Gagarumar Zanga Zanga

  • Kungiyar kwadago ta ƙasa watau NLC ta shirya gagarumar zanga-zanga kan ƙarin kuɗin kira da sayen data a Najeriya
  • NLC ta sanya ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu, 2025 domin gudanar da wannan zanga-zanga a faɗin ƙasar nan
  • Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta hannun hukumar sadarawa NCC ta amince da ƙarin kuɗin sadarwa da 50%

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - A wani yunkuri na dakile karin kudin amfani da layukan sadarwa da aka shirya yi da kashi 50%, kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shirya zanga-zangar gama gari.

Ƙungiyar NLC ta yanke shawarar fita kan tituna zanga-zangar adawa da ƙarin kuɗin kira a faɗin ƙasar nan ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu, 2025.

Yan kwadago.
NLC ta shirya gagarumar zanga zanga kan karin kudin waya a Najeriya Hoto: NLC
Source: Facebook

Rahotan Vanguard ya nuna cewa an cimma matsaya kan yin zanga-zanga ne a taron da ya gudana na kwamitin gudanarwa (NAC) na NLC a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta shirya gagarumar zanga-zanga

NLC ta ce manufar wannan zanga-zanga ita ce aika sako mai karfi ga gwamnati cewa ma'aikata ba za su amince da karin kudin kiran waya da sayen data ba.

Ƴan kwadagon sun ce wannan ƙarin da ake shirin yi zai kara dagula matsin tattalin arziki da ake fuskanta a fadin kasar nan.

A baya, NLC ta yi fatali da karin kudin sadarwa da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi ta hannun hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ranar 22 ga Janairu.

A cewar NLC, amincewa da karin kudin kira a irin wannan lokaci da ma’aikata da talakawa ke fama da wahala da matsin tattalin arziki babbar barna ce ga jin dadinsu.

Kungiyar NLC ta yi fatali da ƙarin kuɗin

A cikin wata sanarwa mai taken "Karin kudin sadarwa da kashi 50 cikin 100: Nauyi mai tsanani", Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

"NLC ta yi Allah wadai da amincewar da Gwamnatin Tarayya ta yi ta hannun NCC na karin kudin sadarwa da kashi 50 cikin 100.
"Wannan mataki, a irin wannan lokaci da ma’aikata da talakawa ke fama da matsin rayuwa illa ce ga walwalarsu, kuma tamkar an miƙa su ne ga buƙatun kamfanoni.
"Harkokin sadarwa suna da muhimmanci a rayuwar yau da kullum kamar aiki da samun bayanai. Matsakaicin ma’aikacin Najeriya na kashe kimanin kashi 10 cikin 100 na albashinsa a kan kudin sadarwa.

Ƙarin kuɗin kira zai matsawa ƴan Najeriya

Shugaban NLC ya ƙara da cewa a yanzu da ƙaramin ma'aikaci ke samun akalla N70,000, yana kashe abin da bai gaza N7,000 ba a ɓangaren sadarwa.

"Wannan karin yana nuna yadda gwamnati ke fifita ribar manyan kamfanoni fiye da jin dadin 'yan kasa," in ji shi.

Sakamakon haka ne kungiyar kwadagon ta sanar da cewa za ta mamaye tituna domin zanga-zaɓgar adawa da karin kudin kira ranar Talatar makon gobe, The Nation ta kawo labarin.

NLC ta ba Tinubu shawara kan haraji

A wani labarin, kun ji cewa NLC ta buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauya tunani sannan ya janye kudirin gyaran haraji da ke gaban Majalisa.

Kara karanta wannan

An gano abin da zai jefa 'yan Najeriya miliyan 13 a talauci a 2025, an gargadi gwamnati

Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero ya ce ya kamata Tinubu ya saurari koken ƴan Najeriya, ya janye kudirin a kara zama a kansa kafin maida shi Majalisa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262