Fada Ya Barke a cikin Masallacin Legas, Hausawa na Dambe kan Wanda Zai Yi Limanci
- Gwamnati ta rufe masallacin Hausawa na garin saboda rikicin shugabanci da ya barke bayan rasuwar babban limamin masallacin
- Bangarori uku ne ke takara kan limancin; iyalan mamacin, bangaren Sarkin Hausawan Agege, da na Na'ibi wanda ke ikirarin shi ya dace
- Shugaban karamar hukumar Agege ya ce rufe masallacin na wucin gadi ne, kuma za a yi zama don sulhunta bangarorin da ke rikicin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Kwanaki uku kenan da rikici a kan wanda zai yi limanci ya sa an rufe babban masallacin Hausawa na garin Agege, da ke jihar Legas.
Karamar gukumar Agege, karkashin jagorancin Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi, ta rufe masallacin ne a ranar Asabar saboda rikicin limanci.

Asali: Getty Images
An rufe masallacin Legas kan limanci
Rikicin limancin ya barke bayan rasuwar babban limamin Hausawa na Agege, Sheikh Sharif Habib Abdul-Majid, a makon da ya gabata, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga masu ibada a cikin masallacin suna ba hammata iska.
Bangarori uku ne ke takarar limancin a yanzu; iyalan mamacin da magoya bayansu, Sarkin Hausawan Agege da magoya bayansa.
Dayan bangaren shi ne na iyalan Na'ibi, wanda ke ganin cewa dole ne na'ibi ya gaji mamacin a matsayin sabon limami.
Rikici ya hana sallar Juma'a a masallacin
Sheikh Mahmud Shafi’i ya shaida wa manema labarai cewa rikicin ya barke ne a ranar Juma’a lokacin da Na'ibi ya so hawa mimbari amma aka hana shi.
An samu tsaikon sallar Juma’a saboda wannan rikici da ya barke tsakanin bangarorin da ke takaddama kan limancin masallacin.
Sakataren sarkin Hausawan Agege, Alhaji Abubakar Ali Na’ibi, ya bayyana cewa sarkin Hausawan ne ke kula da masallacin.
Matsayar da ciyaman din Agege ya dauka
Shaykh Mustapha Imam Danlami, daya daga cikin masu takara, ya shaida wa manema labarai cewa shi ne mataimakin limami, don haka shi ya dace da mukamin.
Lokacin da aka tuntubi dan mamacin, Shaikh Sharif Ismail Habib Abdul-Majid, ya ki magana, yana mai cewa yana cikin zaman makoki.
Shugaban haramar hukumar Agege ya ce rufe masallacin ya zama dole don hana ci gaba da rikicin.
Ya ce zai gayyaci dukkanin bangarorin da ke rikicin domin zama kan teburin sulhu da samar da maslaha.
Ya ce za a bi hanyoyin da suka dace don tabbatar da cewa an cimma zaman lafiya a cikin al’ummar Hausawan Agege.
Limamin Legas ya yiwa Tinubu nasiha
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi sallar Jumu'a a Legas inda limamin masallacin ya yi masa nasiha a kan yin mulki na gaskiya.
Sheikh Ridhwan Jamiu ya tunatar da Shugaba Tinubu cewa akwai ranar hisabi da Allah zai tambaye shi yadda ya gudanar da mulkinsa, don haka ya kamanta adalci.
Asali: Legit.ng