'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Shugaban Karamar Hukuma a Katsina, Sun Yi Barna

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Shugaban Karamar Hukuma a Katsina, Sun Yi Barna

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a gidan shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi
  • Ƴan bindigan a yayin harin sun hallaka wani jami'in ƴan sanda da ke aiki a gidan shugaban ƙaramar hukumar da ke Katsina
  • Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar cafke mutum uku da ake zargin suna da hannu a harin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina a ranar Talata.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a gidan shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi, Maharazu Dayi.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun kai hari gidan ciyaman a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda a Katsina

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wani jami'in ɗan sanda mai aiki a gidan shugaban ƙaramar hukumar, mai suna Shamsudeen Lawal, ya rasa ransa a sakamakon harin.

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa jami'in ɗan sandan ya mutu ne lokacin da ƴan ta'addan da ke ɗauke da makamai suka farmaki gidan shugaban ƙaramar hukumar, amma suka gamu da tirjiya.

Ko da yake shugaban ƙaramar hukumar da iyalinsa suna cikin gidan lokacin da aka kai harin, sun samu damar tserewa cikin ƙoshin lafiya.

Mazauna yankin sun bayyana cewa harin ya janyo an lalata wasu sassan gidan shugaban ƙaramar hukumar.

Akwai rashin tsaro a wasu ƙananan hukumomin Katsina

Yankin Malumfashi yana daga cikin wuraren da ke fuskantar matsalar rashin tsaro a jihar Katsina.

Rahotanni na nuna cewa hare-haren ƴan ta'adda, ciki har da kashe-kashe, sace-sace, da satar dabbobi, sun zama ruwan dare a wasu ƙananan hukumomi, musamman waɗanda ke kusa da dazuzzuka.

Gwamnatin jihar ta Katsina ta samar da rundunar KSCWC wacce ke aiki da sauran hukumomin tsaro domin yaƙi da ƴan bindiga.

Harin na ranar Talata ya haifar da damuwa kan tasirin matakan da aka ɗauka da kuma buƙatar ƙara inganta dabarun magance matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Ƴan sanda sun yi ƙarin haske kan harin

Legit Hausa ta yi yunƙurin tuntuɓar mai magana da yawun ƴan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin rundunar ƴan sandan ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce jami'in ya rasu bayan an garzaya da shi zuwa asibiti sakamakon raunin da ya samu.

Ya bayyana cewa jami'an rundunar sun samu nasarar cafke mutum uku da ake zargin suna da hannu a harin da aka kai.

"Mun yi nasarar kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a wannan aika-aika, sannan muna ci gaba da gudanar da bincike idan akwai wani ƙarin bayani za mu fitar."

- DSP Abubakar Sadiq Aliyu

Kankara: Ƴan bindiga sun buƙaci kuɗin fansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindigan da suka sace ma'aikatan lafiya a babban asibitin ƙaramar hukumar Kankara, sun buƙaci a ba su kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

Miyagun ƴan bindigan sun buƙaci a ba su Naira miliyan 540 kafin su sako mutanen da suka sace bayan sun farmaki asibitin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng