Barawon da Ya Sace Kayan N500, 000 a Masallaci Ya Shiga Hannu

Barawon da Ya Sace Kayan N500, 000 a Masallaci Ya Shiga Hannu

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Ogun ta sanar da cafke wani matashi mai suna Idowu Kehinde mai shekaru 35 bisa zargin satar kayan masallaci
  • Rahotanni sun anuna cewa an kama matashin bayan ya sayar da fankokin masallaci takwas da tagogi hudu da darajarsu ya kai N520,000
  • Bayan bincike, jami'an 'yan sanda sun gano wani mutum da ake zargi ya saye kayan da aka sace a masallacin, kuma an shirya gurfanar da shi a kotu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mutum mai suna Idowu Kehinde, mai shekaru 35, bisa laifin kutsawa wani masallaci a yankin Agbado.

Rahotanni da Legit ta samu bayan kama matashin sun nuna cewa ya sace kayan masallacin da kudinsu ya kai N520,000.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Jihar Ogun
An kama barawon da ya sace kayan masallaci a Ogun. Hoto: Legit
Asali: Original

Bayanan da Punch ta wallafa sun nuna cewa mutumin ya haura katangar masallacin Mapara Moboluwaduro ne inda ya kwashe fankokin sama takwas da tagogin karfe hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama barawo a masallaci

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta tabbatar da kama wanda ake zargi, inda ta ce ya amsa laifinsa bayan an yi masa tambayoyi.

A cewar Omolola Odutola:

"A ranar 27 ga watan Janairu, da misalin ƙarfe 9 na safe, an samu rahoto cewa wani mutum mai suna Idowu Kehinde, mai shekaru 35, ya haura katangar masallaci a Agoro a Adiyan,
"Mutumin ya sace fankokin sama takwas da tagogin karfe hudu da kudinsu ya kai N520,000."

Ta ƙara da cewa an samu buhun da ke ɗauke da wasu kayan sata, kuma an shirya gurfanar da wanda ake zargi a kotu.

An kama wanda ya saye kayan masallaci

Bayan kama wanda ake zargi, ‘yan sanda sun gano cewa ya sayar da kayayyakin ga wani mutum mai suna Awal Yusuf, mai shekaru 31.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

Kakakin 'yan sanda ta bayyana cewa:

"An kama wanda ake zargi kuma ya amsa cewa ya sayar da kayayyakin ga wani mai suna Awal Yusuf.
"Mun kuma gano wasu kayan satar a hannun wanda ya saye kayan masallacin, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu nan bada daɗewa ba."

Yadda ake sace sace a jihar Ogun

Bayananai sun nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake samu irin wannan sata a wuraren ibada a jihar Ogun ba.

Kwanan nan, ‘yan sanda sun kama wani matashi mai shekaru 16 mai suna Ademola Bolu, bisa laifin satar kayan rufin gini da kudinsu ya kai N180,000 a wani coci a Odeda.

Bolu da wasu abokan aikinsa da har yanzu ba a kama su ba, an same su da buhuna biyu cike da kayan da suka sace a cocin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

‘Yan sanda sun bayyana cewa suna ci gaba da bincike domin ganin an cafke sauran miyagun da ke da hannu a cikin satar kayayyakin wuraren ibada a jihar Ogun.

Kano: Izala ta yi magana kan rikicin masallaci

Sai dai shugaban Izala na jihar Kano ya ce a iya abin da suka sani ba a zalunci malamin ba, kuma yana da tabbacin cewa an masa adalci.

Shi wanda ya gina masallacin, Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi, ya ce sharrin shaiɗan ne ya jawo rikicin kuma ya yi nasiha ga dukkan bangarorin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel