'Yan Sa kai Sun Yi Ta'asa a Neja, 'Yan Sanda Sun Yi Caraf da Su

'Yan Sa kai Sun Yi Ta'asa a Neja, 'Yan Sanda Sun Yi Caraf da Su

  • Ana zargin wasu jami'an tsaro na ƴan sa-kai da aikata laifin kisan gilla a ƙaramar hukumar ta jihar Neja a Arewa
  • Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta samu nasarar cafke ƴan sa-kan guda uku waɗanda ake zargi da aikata laifin
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da cafke mutanen, ya bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran masu hannu a lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta kama wasu ƴan sa-kai guda uku, Habibu Usman, Tanko Abara da Maigero Abdullahi, dukkansu mazauna garin Tunga-Galadima da ke ƙaramar hukumar Rijau.

Rundunar ƴan sandan ta cafke ƴan sa-kan ne bisa zargin kashe wani mutum mai suna Muhammadu Bello mai shekaru 30, daga garin Awala na ƙaramar hukumar Rijau.

'Yan sanda sun cafke 'yan sa-kai a Neja
'Yan sa-kai sun shiga hannun 'yan sanda a Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Shawulu E. Danmamman, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kawo cikas ga ayyukan 'yan Boko Haram da 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun cafke ƴan sa-kai a Neja

Ya bayyana cewa jami'an ƴan sanda na sashen Kontagora ne suka kama waɗanda ake zargin a ranar 16 ga watan Janairu, 2025.

"An kama waɗanda ake zargin ne bisa laifin kisan gilla ga wani Muhammadu Bello mai shekara 30 na garin Awala, ƙaramar hukumar Rijau."
"Rahotanni sun nuna cewa a ranar 8 ga Disamba, 2024, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, wanda aka kashe ya je shingen binciken ƴan sa-kai da ke Tunga-Galadima tare da babur ɗinsa na Bajaj."
"Marigayin yana dawowa ne daga Kontagora domin zuwa Rijau, tare da kuɗi kimanin N940,000 a hannunsa."
"Tun daga wannan rana ba a sake jin ɗuriyar sa ba, har sai da aka gano gawarsa a cikin daji kusa da shingen binciken ƴan sa-kai a ranar 13 ga watan Janairu, 2025."
"Saboda haka, an fara zargin ƴan sa-kai da laifin, inda aka kama mutum uku daga cikinsu. Daga baya, Habibu Usman ya amsa cewa wani daga cikinsu mai suna Lawal, wanda yanzu haka ya tsere, shi ne ya harbe marigayin a shingen binciken ƴan sa-kan."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana kan cafke Muhuyi Magaji, sun fadi abin da ya faru

- Shawulu E. Danmamman,

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da kokarin kama sauran mutane uku da ake zargi da hannunsu a cikin lamarin, watau Lawal, Jibrin da Bako.

Ƴan sanda sun kama masu ba ƴan ta'adda babura

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Neja ta samu nasarar cafke wasu masu samar da babura ga ƴan ta'addan Boko Haram da ƴan bindiga.

Mutanen da ake zargin dai suna samar da babura ne ga ƴan ta'addan Boko da ƴan bindiga a jihohin Neja da Kaduna domin su riƙa yin amfani da su.

Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke mutanen da ake zargin ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu a ƙaramar hukumar Suleja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel