"Ba Kamar Tinubu ba": Amaechi Ya Fadi Yadda Ya Shirya Samar da Sauki ga Talaka

"Ba Kamar Tinubu ba": Amaechi Ya Fadi Yadda Ya Shirya Samar da Sauki ga Talaka

  • Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi
  • Amaechi wanda ya amince cewa dole ne a cire tallafin, ya nuna alamar tambaya kan shirin gwamnatin Tinubu kafin daina biyan tallafin
  • Tsohon ministan sufurin ya bayyana cewa da a ce ya samu nasarar zama shugaban ƙasa, da ya bi wata hanya daban wajen soke tsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya bayyana abin da ya yi niyyar yi da ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa da shi aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa, da ya tafiyar da cire tallafin man fetur ta wata hanya daban.

Amaechi ya magantu kan cire tallafin fetur
Amaechi ya fadi shirinsa kan cire tallafin fetur Hoto: @officialABAT, @ChibuikeAmaechi
Asali: Twitter

Amaechi ya nuna alamar tambaya ga Tinubu

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana hakan ne a wajen wani taro a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaechi ya jaddada muhimmancin samar da gidaje da samar da ayyukan yi domin rage tasirin cire tallafin man fetur.

Rotimi Amaechi, wanda ya riƙe muƙamin ministan sufuri daga 2015 zuwa 2022, ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC a 2022 amma ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa cire tallafin man fetur abu ne da dole kowanne shugaban ƙasa ya aiwatar, amma ya nuna alamar tambaya kan dacewar lokacin da aka cire shi da kuma shirin gwamnatin Tinubu ta kafin sanar da cire tallafin.

Wane shiri Amaechi yake da shi?

“Babu wani mutum da zai zama shugaban ƙasa da ba zai cire tallafin ba. Abin da ban sani ba shi ne wane lokaci ne mafi dacewa don cire shi? Wane irin shiri gwamnatin Tinubu ta yi kafin sanar da cire tallafin?"

- Rotimi Amaechi

Ya bayyana cewa iyalinsa sun tambaye shi abin da zai yi daban da ace shi ne ke kan madafun iko, sai ya amsa da cewa:

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

"Zan cire tallafin, amma ba zan cire shi ba tare da samar da gidaje ba. Me yasa? Domin kuɗin da za a adana daga cire tallafin da kuma faɗuwar darajar Naira, za a iya amfani da su don gina gidaje tsakanin 200,000 zuwa 300,000."
Amaechi ya bayyana cewa irin wannan tsari ba kawai zai magance matsalar ƙarancin gidaje ba, zai yi tasiri wajen samar da ayyukan yi ga mutane da dama.
“Idan ka gina gidaje tsakanin 200,000 zuwa 300,000 a jihohi, yawan ayyukan da za ka samar nawa ne? Aƙalla za ka samar da birkiloli, 300,000, kafintoci 300,000 da masu gyaran bututun ruwa 300,000."
"Idan ka aiwatar da wannan tsari, me za ka samu? Ka samar da kuɗaɗe a hannun jama’a."

- Rotimi Amaechi

Rotimi Amaechi ya kuma koka kan yadda gibin dake tsakanin attajirai da talakawa ke ƙaruwa a Najeriya, ya bayyana rashin samun ƴan tsaka-tsakiya a cikin al’ummar ƙasar nan a matsayin babban ƙalubale.

Kara karanta wannan

"Ana saye ra'ayin 'yan adawa da N50m": Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'aziyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika da saƙon ta'aziyya ga gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Shugaban ƙasan ya yi wa Gwamna Seyi Makinde ta'aziyya bayan ɗan uwansa ya riga mu gidan gaskiya, ya yi alhini tare da yin addu'a a gare shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel