Watanni da Aure, Diyar Mataimakiyar Gwamna Ta Yi Bankwana da Duniya yayin Naƙuda
- An shiga jimami yayin da diyar mataimakiyar gwamnan Akwa Ibom ta riga mu gidan gaskiya yayin haihuwa
- Marigayiyar mai suna Mrs Blessing ta rasu ne a birnin Port Harcourt a yau Talata 28 ga watan Janairun 2025
- Marigayiyar, wadda aka yi wa aure watanni bakwai da suka gabata, ta rasu a wani asibiti a jihar Rivers
- Manyan jami’an gwamnati da abokan arziki suna ci gaba da aikewa da sakonnin ta’aziyya ga iyalinta a wannan lokaci na bakin ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Uyo, Akwa Ibom - Mataimakiyar Gwamnan jihar Akwa Ibom, Dr. Akon Eyakenyi ta tafka babban rashi a rayuwarta.
Dattijuwar ta rasa yarta mai suna Mrs Blessing a birnin Port Harcourt yayin nakuda a jihar Rivers.
Uwar gidan gwamnan Akwa Ibom ta rasu
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa marigayiyar ta yi aure watanni bakwai da suka gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Allah ya karbi rayuwar uwar gidan gwamnan Akwa Ibom, Fasto, Patience Umo Eno a wani asibiti bayan fama da rashin lafiya.
Kwamishinan yada labarai, Mista Ini Ememobong ya fitar da sanarwar rasuwar inda ya ce ta rasu ne a ranar Alhamis, 26 ga Satumba.
Duk da rasuwar matarsa, sanarwar ta ce Gwamna Umo Eno ya ba al'ummar Akwa Ibom tabbacin jajircerwarsa wajen yi masu hidima.
Diyar mataimakiyar gwamna ta rasu
An tabbatar da cewa marigayiyar ta rasu ne sakamakon haihuwa a wani asibiti da ke birnin Port Harcourt a jihar Rivers.
Manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da abokan arziki sun aike da sakonnin ta’aziyya ga iyalinta a wannan lokaci mai cike da bakin ciki.
Bidiyo da hotunan bikin auren Blessing da mijinta, Olumuyiwa Adewumi, a wurin ibada na Int'l Worship Centre da ke Uyo, babban birnin jihar, sun ci gaba da mamaye shafukan sada zumunta.
Martanin yan Najeriya kan rasuwar
Haka kuma, ana ta wallafa gaisuwa da jimami a shafukan sada zumunta, bayan mummunan al’amarin da ya faru watanni kalilan bayan rasuwar matar gwamnan.
Wani mai amfani da X, @IdiongoUdoh_ ya bayyana wannan al’amari a matsayin abin bakin ciki matuka.
@EstherUmo10:
"Yake Blessing, cikin alhin da kaduwa, nake ce miki sai wata rana.
"Ina mika ta'aziya ga mahaifiyarki (Mataimakiyar Gwamnan Jihar Akwa Ibom), mijinki mai kaunarki, da kuma abokiyarki mai shekaru 17, Eby.
"Kai hakika kin kasance mai kyakkyawar zuciya."
@Sifon_Bassey:
"Ina mika ta’aziyyata ga mataimakiyar Gwamnan Jihar Akwa Ibom kan rashin ‘yarta.
"Rashin yaro abu ne mai matukar bakin ciki.
"Wannan abin takaici ne sosai. Allah Ya ba wa iyali ƙarfin jure wannan babban rashi."
Tsohon Minista a Najeriya ya kwanta dama
A baya, kun ji cewa tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Janar Jeremiah Useni, ya rasu a yau Alhamis, 23 ga Janairu, 2025, bayan fama da jinya mai tsawo.
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga danginsa, Sojojin Najeriya, Jihar Filato, da kasa baki daya.
Janar Useni ya yi ayyuka masu daraja a rayuwarsa, ciki har da jagoranci, siyasa, da kokarin tabbatar da zaman lafiya musamman a Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng