Wata Tankar Man Fetur Ta Sake fashewa a jihar Neja, ana fargabar mutane sun mutu

Wata Tankar Man Fetur Ta Sake fashewa a jihar Neja, ana fargabar mutane sun mutu

  • Ana fargaba mutane hudu sun mutu yayin da wata tankar tankar man fetur ta sake fashewa a garin Kusogbogi da ke jihar Neja
  • Rahoto ya ce tankar man ta kama wuta yayin da take kokarin wuce wata babbar mota, wanda ya janyo fashewarta da wata mota
  • Majiya ta ce gudun wuce sa'a da kwacewar sitiyari ne ya haddasa hatsarin har ta kama da wuta yayin da ake jiran rahoton NSEMA

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Wata tankar man fetur ta sake fashewa a jihar Neja 'yan kwanaki kadan bayan da tankar mai ta fashe tare da kashe mutane da da dama a Dikko.

Sabuwar fashewar tankar man ta faru ne a garin Kusogbogi, wani gari da ke kan iyaka da kananan hukumomin Agaie da Lapai.

Kara karanta wannan

Jirgin Max Air da ya tashi daga Legas zuwa Kano ya yi hatsari, an samu karin bayani

Majiya ta yi bayanin yadda tankar man fetur ta fashe a jihar Neja
Tankar mai ta sake fashewa a jihar Neja inda ake fargabar mutane 4 sun mutu. Hoto: AMINU ABUBAKAR
Asali: Getty Images

Tankar mai ta sake fashewa a Neja

Rahoton TVC News ya nuna cewa tankar man ta fashe ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani da lamarin ya faru a kan idonsa, ya shaida cewa akwai mutane hudu da suke cikin tankar a lokacin da ta fashe, kuma ana fargabar sun mutu.

Har zuwa yanzu dai hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ba ta fitar da rahoto a hukumance game da fashewar tankar ba.

Mazauna Neja ta fadi yadda tankar ta fashe

Sai dai kuma wani sabon rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar, ya nuna cewa tankar ta fashe ne da misalin karfe 6:00 na yammacin Talata.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa babu wanda ya rasu a wannan mummunan iftila'in da ya faru.

Wani mazaunin Lapai, Mallam Mahmud Abubakar, ya ce tankar ta kama da wuta ne yayin da take kokarin wuce wata babbar mota a kan hanyar.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

Abubakar ya ce a nan wajen ne wata tankar mai ta fashe a makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Ya ce fashewar tankar na ranar Talata, ya faru ne sakamakon gudun wuce sa'a da kuma wacewar sitiyari, kuma ta kama da wuta bayan ta bugi motar da ke ajiye a gefen titi.

Tankar mai ta fashe, mutane 11 sun mutu

A wani labarin, mun ruwaito cewa an samu asarar rayuka bayan fashewar wata tankar mai a jihar Enugu, dake yankin Kudu maso Gabas na Najeriya.

Fashewar tankar ɗauke da man fetur ta faru ne sakamakon matsalar birki, wanda ya jawo tankar ta kife a kan titi sannan ta kama da wuta.

Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa tare da alƙawarin ɗaukar matakai don hana aukuwar irin wannan iftila'i nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel