Malami Ya Faɗi Jihohi 8 da Ƴan Bindiga Ke Shirin Kai Hari, Ya Ce Rayuwar Sarki na cikin Haɗari

Malami Ya Faɗi Jihohi 8 da Ƴan Bindiga Ke Shirin Kai Hari, Ya Ce Rayuwar Sarki na cikin Haɗari

  • Fitaccen malamin coci a Najeriya, Primate Ayodele ya buƙaci sojoji su tashi tsaye su kawo karshen ayyukan ta'addanci a Najeriya
  • Ayodele, wanda ya saba hasashen abin da zai faru, ya ce ya hango jihohi takwas da ƴan bindiga ke shirin kai hare-hare a Arewa
  • Ya buƙaci shugabannin hukumomin soji su daƙile wannan yunkuri na ƴan ta'adda a faɗin kasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Ayodele, ya yi gargadi kan yiwuwar kai sababbin hare-haren ta’addanci a wasu jihohin Najeriya.

Fitaccen limamin cocin wanda ya yi ƙaurin suna wajen hasashen abubuwan da za su faru, ya bukaci sojojin Najeriya su tashi tsaye su kare rayukan al'umma.

Primate Ayodele.
Primate Ayodele ya bayyana jihohin da yan ta'adda ke shirin kai sababbin hare-hare a Najeriya Hoto: Primate Ayodele
Asali: Facebook

Malamin majami'ar ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 28 ga watan Janairu, 2025, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayodele ya faɗi jihohi 8 da ya hango matsala

Primate Ayodele ya lissafa jihohin da yake hasashen ƴan bindiga za su kai hare-haren ta'addanci wanda suka haɗa da Nasarawa, Gombe, Filato, Kaduna, Bauchi, Benuwai, Abuja da Kogi.

Babban malamin addinin ya bukaci hafsan hafsoshin tsaro na ƙasa, Christopher Musa da shugaban rundunar sojojin ƙasa su tashi tsaye.

A cewarsa, ya kamata dakarun sojoji su kasance a ankare domin daƙile waɗannan hare-hare da ake shirin kai wa kan bayin Allah a jihohin da ya ambata.

Ƴan ta'adda na shirin kai wa sarki hari

Bugu da kari, Primate Ayodele ya yi gargadi kan wani shirin da ƙungiyar ESN, mayakan kungiyar ƴan aware ke yi na kai hari a yankin Kudu maso Gabas.

Ya ce mayaƙan ESN, sashen dakarun ƙungiyar ta'addanci ta IPOB na shirin kai munanan hare-hare musamman kan wani sarki da bai faɗi sunansa ba.

Limamin cocin ya jaddada bukatar daukar matakan tsaro da tsara ingantattun dabaru domin hana wadannan hare-hare da kuma kare rayukan ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

Ayodele ya buƙaci sojoji su daƙile shirin

“Ƴan bindiga za su faɗaɗa kai hare-haren ta’addanci zuwa jihohin Nasarawa, Gombe, Filato, Kaduna, Bauchi, Benuwai, Abuja da Kogi.
"Ya kamata babban hafsan tsaro da hafsan rundunar sojin ƙasa su tattauna tare da tsara dabaru; lokaci ya yi da za a kawar da ‘yan ta’adda a kasar nan."
“Dukkansu suna da kwarewa, bai kamata su bari wadannan ‘yan ta’adda su lalata tarihin nasarorinsu da mutuncinsu ba.

- Primate Ayodele.

Limamin cocin ya ƙara da cewa:

"Kungiyar ESN kuma tana shirin kai hari a Kudu maso Gabas, wannan babban gargadi ne domin suna da niyyar hallaka mutane da dama, ciki har da wani sarki."

Ƴan ta'adda sun kashe kwamandan soji a Borno

A wani labarin, kun ji cewa ƴan ta'addan kungiyar ISWAP/Boko Haram kashe kwamandan rundunar soji da wasu dakaru a Borno da ke Arewa maso Gabas.

An ruwaito cewa maharan sun kai wannan faramki ne a cikin motocik yaƙi, sun tafka barna a sansanin sojin Malam Fatori a jihar Borno.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel