Tirkashi: Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Maka Shugaban APC a Kotu, Yana Neman N500m
- Dan takarar gwamnan Edo karkashin jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo ya maka shugaban jam'iyyar APC na jihar kotun Legas
- Ighodalo na karar Jarret Tenebe kan zargin bata masa suna ta hanyar zarginsa da satar kudin gwamnati a wani bidiyo da ya bazu
- Dan takarar gwamnan na neman kotu ta sanya shugaban APC ya biya shi diyyar N500m, ya janye kalamansa da kuma ba shi hakuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Dakta Asue Ighodalo, dan takarar PDP a zaben gwamnan Edo na 2024, ya maka shugaban APC na jihar, Jarret Tenebe, a kotu kan zargin bata suna.
Ighodalo na neman diyyar N500m, yayin da yake ikirarin cewa kalaman Tenebe sun yi matukar bata masa suna da cutar da martabarsa a idon jama’a.
Dan takarar gwamna ya yi karar shugaban APC
Dan takarar gwamnan ya shigar da karar ne a babbar kotun jihar Lagos da ke Tafawa Balewa Square, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa Ighodalo na neman a kotun ta tursasa Tenebe ya biya shi diyya, ya janye zargin, sannan ya bashi hakuri a fili.
Ighodalo ya shigar da karar ne sakamakon wani faifan bidiyo da ya shahara a soshiyal midiya a ranar 10 ga Disamba, 2024, inda yake zargin Tenebe ya bata masa suna.
Abin da ya jawo aka maka shugaban APC a kotu
A cikin bidiyon, an ji Tenebe yana zargin Asue Ighodalo da karbar rashawa tare da karkatar da kudaden gwamnati, inda yake cewa:
“Asue Ighodalo ba zai sake irin wannan kuskuren ba saboda ya riga ya saci biliyoyin Naira a baya.”
Wannan kalami ya biyo bayan rawar bakin da Monday Okpebholo ya yi yayin da yake gabatar da kasafin kudin Naira biliyan 605 a gaban majalisar dokokin Edo.
Kafin shigar da karar, Ighodalo, ta hannun lauyansa daga ofishin Banwo da Ighodalo, ya tura takardar gargadi ga Tenebe a ranar 11 ga Disamba, 2024, yana neman ya janye kalaman tare da neman afuwa cikin kwanaki bakwai.
Edo: Shugaban APC ya kare kansa
Sai dai, Tenebe, ta hannun lauyansa Dakta Blessing Agbomhere, ya musanta zargin bata sunan dan takarar gwamnan kuma ya ki ba da hakurin.
Barista Agbomhere ya mayar da martani ga takardar gargadin, yana mai cewa wanda yake kara bai taba bata sunan Ighodalo ba, don haka ba zai ba shi hakuri ko janye maganarsa ba.
Ya kara da cewa idan har Ighodalo ya dage kan cewa sai ya je kotu, to za su dogara da rahoton kwamitin karbo motocin jihar Edo domin kare wanda suke kara.
Haka zalika, Agbomhere ya ambaci rahoton farko na kwamitin binciken dukiyar jihar Edo, wanda a cewarsa ya zargi Ighodalo da aikata laifin da Tenebe ya zarge shi.
Kotu ta sanya ranar fara sauraron karar
A karar da ya shigar, Ighodalo ya ce maganganun da Tenebe ya yi a bidiyon da aka watsa ya bata masa suna da kuma jefa shi cikin jin kunyar jama'a.
Ya bayyana cewa tun bayan sakin bidiyon, ya rika samun korafe-korafe daga abokan aiki, abokan kasuwanci, da sauran masu ruwa da tsaki, wanda hakan ya jefa shi cikin damuwa.
“Ba tare da tantama ba, wannan lamarin ya jefa wanda muke karewa cikin damuwa, bakin ciki da kuma shiga kunya,” a cewar takardar lauyoyin Ighodalo.
An ruwaito cewa Mai shari’a A.O. Opesanwo na babbar kotun jihar Legas ya sanya ranar 5 ga Maris, 2025, domin fara sauraren karar.
Wanene Dokta Asue Ighodalo?
A wani labarin, mun rahoto cewa Asue Ighodalo babban lauya ne wanda ya bude Banwo & Ighodalo, daya daga cikin manyan ofisoshin lauyoyi na Najeriya.
Asue Ighodalo ya zama dan takarar PDP a zaben gwamnan Edo, amma ya sha kaye a hannun dan takarar APC a zaben jihar na ranar Asabar, 21 ga Satumbar 2024.
Asali: Legit.ng