Mazauna Jigawa za Su Fara Ganawa da Gwamnansu Kai Tsaye

Mazauna Jigawa za Su Fara Ganawa da Gwamnansu Kai Tsaye

  • Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, zai fara wani shiri na zagayawa cikin kananan hukumomi domin tattaunawa da mazauna yankuna
  • Garba Muhammad, mai ba gwamna shawara kan kafafen yada labarai na zamani, ya bayyana cewa wannan shirin shi ne karo na farko a Jigawa
  • Shirin na gwamna zai hada shugabannin kungiyoyi da jagororin al’umma a kowace karamar hukuma, domin mika bukatunsu ga gwamna kai tsaye

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa zai fara zagayawa domin ya tattauna da mazauna jihar a kananan hukumominsu domin inganta harkar gudanar da al'umma.

Mashawarcin gwamnan a kan kafafen yada labarai na zamani, Garba Muhammad ya shaidawa Legit cewa an fito da sabon tsarin domin gwamna ya ji daga bakin mutanen da ya ke mulka.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun cafke mai safarar makamai daga Nijar zuwa Najeriya

Jigawa
Gwamnan Jigawa zai fara ganawa da jama'a Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Garba Muhammad ya ce gwamna Namadi ya amince da ƙaddamar da shirin domin jin ra'ayoyin jama'a, ƙorafe-ƙorafe, da shawarwari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwamnan Jigawa na ganawa da jama'a

Garba Muhammad ya bayar da tabbbacin cewa sabon tsarin zai inganta tsarin gudanar da gwamnati, tare da ba gwamna damar sanin ainihin abin da jama’a ke bukatar a yi masu.

Ya kara da cewa;

'Tun kafin shi mai girma gwamna ya hau kujerarsa, akwai daftarin bukatun jama'a da ya karba daga kungiyoyi da shugabannin al'umma.
"Kuma shi wannan duka daftari, matsaloli ne al'umma da irin abubuwan da su ke so. Tun da shi ya na yin tsari ne na ci gaban kauyuka.

Ya kara da cewa garuruwa daban-daban su na da abubuwa da su ke bukata, koma kowane zai iya bambanta da na sauran.

Yadda gwamnan Jigawa zai gana da jama'arsa

Kara karanta wannan

Bayan an nemi ya fice daga PDP, gwamna ya ɗauko mutum 8 ya ba su muƙamai

Gwamna Umar Namadi zai fara tattaunawa da jama'a a wani shiri da za a hada shugabannin kungiyoyi da sauran jagororin al'umma a kananan hukumomi daban-daban.

Mai ba gwamnan shawara a kan kafafen yada labaran zamani, Garba Muhammad ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da za a gudanar da irin wannan shiri a Jigawa.

Garba Muhammad ya ce:

"Ba a taba yinsa ba, abu ne na farko, fara shin da za a yi, zai dauki tsawon lokaci ana kewaye wadannan kananan hukumomi. Idan an kammala kuma shi ne zai bayar da kofa ta yiwuwar a ci gaba da yi, a sake yin sa saboda yanayin ra'ayin mutane da za a samu.

Hadimin Gwamnan ya bayar da tabbacin wannan sabon tsarin zai taimaka wajen bunkasa samar da ayyukan da al'umma su ke bukata, a wuraren da su ke bukata, da kuma mika kokensu kai tsaye ga gwamnati.

Gwamnatin Jigawa ta fitar da tsarin ilmi kyauta

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya nada sabbin mukamai, an sauya wa wasu wurin aiki a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa a wani yunƙuri na tabbatar da cigaban ilimi da ƙarfafa mata, Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da wani sabon tsari na bayar da ilimi kyauta ga duk mata yan asalin jihar.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Farfesa Isa Chamo, ya bayyana cewa wannan tsari yana da nufin kawar da cikas da ke hana yara mata samun ilimi, musamman rashin kuɗi da ya zama cikas ga jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.