Gwamnatin Kano Ta Yi Kuskuren Ingiza wa Wani Jami'inta Maƙudan Kuɗi, Ya Dawo da Su
- Mataimakin Manajan Darakta na hukumar REMASAB, Alhaji Muktar Lamir Hassan ya maida kuɗi sama da N4.7m da aka tura masa bisa kuskure
- Babban jami'in gwamnatin ya ce da farko ya ɗauka albashinsa na watan Janairu, 2025 ne amma da ya sake dubawa sai ya ga kudin sun yi yawa
- Ya ce a matsayinsa na ɗan Kano mai alfahari da jiharsa, ya maida kudin ne domin gwamnati ta yi amfani da su a hanyar da ta dace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Shara da Muhalli ta Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Mukhtar Lamir Hassan, ya yi abin a yaba masa.
Alhaji Muktar Lamir ya mayar da kuɗi sama da Naira miliyan 4.7 da aka tura cikin asusun bankinsa bisa kuskure daga gwamnatin jihar Kano.
![Gwamna Abba Kabir Yusuf. Gwamna Abba Kabir Yusuf.](https://cdn.legit.ng/images/1120/4f2c3c88161e5f2b.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Babban jami'in gwamnatin ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai bayan ya mayar da kudin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta tura kudi bisa kuskure
Mukhtar Lamir Hassan ya bayyana cewa a farko ya dauka kudin albashinsa ne na watan Janairu, 2025.
Sai dai, bayan da ya duba jimullar kudin da ke cikin asusun, ya gane cewa adadin ya zarce albashinsa na wata-wata fiye da kashi 85%.
An ruwaito cewa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada shi muƙamin, mutumin ya fuskanci jinkirin albashi na watanni kafin a biya shi gaba ɗaya har da na watannin da ya biyo bashi a Disamba 2024.
A watan Janairu 2025, gwamnati ta sake aika masa da adadin kudin da aka tura masa a baya ba tare da hada masa da albashin watan Janairu ba.
Jami'in gwamnatin ya mayar da kudin
"Na gane kuskure ne saboda kudin sun yi daidai da albashin da aka biya ni a Disamba, 2024, babu albashin Janairu a ciki.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/663cd0e21747d55f.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Wani katafaren otal da kamfanoni 4 sun shiga gonar gwamnatin Kano, an ɗauki mataki
"Don haka, nan take na sanar da Ma'aikatar Kudi da Ofishin Akanta Janar,” in ji Lamin Hassan.
Ya ce daga nan sai ya mayar da dukkan kudin tare da samun takardar shaidar mayarwa, wanda ya gabatar ga ma’aikatar kudi ta jihar Kano a matsayin hujja.
'Abin da ya sa na mayar da kuɗin'
Alhaji Mukhtar Lamir Hassan ya bayyana cewa ya mayar da kuɗin ne saboda ba haƙƙinsa ba ne.
“A lokacin da na mayar da sama da naira miliyan 4.7, kudin da ke asusuna bai kai kashi 10% na wannan adadin ba, kuma ban samu albashina na Janairu ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa, a matsayinsa na ɗan asalin Kano mai alfahari da jiharsa, haƙƙi ne da ya rataya a wuyansa ya maida kuɗin ga gwamnati domin a yi amfanin da ya dace da su.
Gwamnatin Kano ta rufe otal da kamfanoni 4
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin Kano ta garƙame babban otal da ofisoshin wasu kamfanoni hudu saboda taron bashin da aka biyo su na haraji.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/8a0490f9c7ce84d9.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Hukumar tara haraji ta Kano watau KIRS ta ce sai da aka tunatar da su biyan kuɗin amma suka yi kunnen ƙashi, suka ƙi biyan bashin da ake binsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng