Harin Ta'addanci: 'Yan Sanda Sun Fadi Nasarorin da Suka Samu a Kano
- Rundunar ƴan sandan jihar ta yi ƙarin haske kan gargaɗin da ta yi kan yiwuwar kai harin ta'addanci
- Kwamishinan ƴan sandan jihar, Salman Garba Dogo, ya bayyana cewa sun samu nasarar ƙwato kayayyaki ciki har da abubuwan fashewa
- Salman Garba Dogo ya ba da tabbacin cewa jami'an rundunar za su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya yi magana kan gargaɗin harin ta'addanci da rundunar ta yi.
Kwamishinan ƴan sandan ya bayyana cewa rundunar ta kama wani wanda ake zargi tare da ƙwato kayayyaki ciki har da abubuwan fashewa, bayan samun rahoton yiwuwar kai harin ta’addanci a jihar.

Asali: Facebook
Salman Garba Dogo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, a Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanne matakai ƴan sanda suka ɗauka a Kano?
Kwamishinan ƴan sandan ya yi bayani kan matakan da rundunar ta ɗauka don tabbatar da tsaron al’ummar Kano da kuma hana aukuwar duk wani hari.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun tsere daga jihar bayan samun rahoton, inda aka gano ɗaya daga cikinsu ya dawo Kano bayan ya bar jihar.
“Bayan samun rahoton yiwuwar kai harin ta’addanci a Kano, musamman a lokacin bikin Mauludin Tijjaniyya, mun ɗauki mataki na gaggawa, mun sanar da jama’a, kuma mun samar da tsare-tsaren da suka dace don magance lamarin."
“Mun kama mutum ɗaya da ake zargi wanda ya fito daga wata coci, bayan mai masaukinsa, wanda yake da makullin gidansa, ya shiga hannu. Bugu da ƙari, mun ƙwato kayayyaki ciki har da abubuwan fashewa."
- Salman Garba Dogo
Ƴan sanda sun yi kira ga jama'a
Kwamishinan ya jaddada muhimmancin samun bayanai don magance barazanar tsaro, inda ya bayyana yadda suka haɗa kai da masu ruwa da tsaki wajen tsaurara tsaro a lokacin bikin mauludin.
"Da muka samu rahoto game da mauludin Tijjaniyya, mun tura ma’aikata, kuma mun sanar da duk masu ruwa da tsaki. A wani wuri, mun haɗa kai da sashen kula da bama-bamai don tabbatar da tsaron wurin."
- Salman Garba Dogo
Kwamishinan ƴan sandan ya yi ƙarin haske kan ƙalubalen aiki a wurin da siyasa ke tasiri, amma ya tabbatarwa al’ummar Kano cewa suna jajircewa wajen kare jihar.
“A Kano, komai sai an siyasantar da shi, har abincin da muke ci. Amma ina tabbatarwa kowa cewa ni da tawaga ta za mu ci gaba da sadaukar da kanmu wajen tsare wannan jiha."
"Ni ɗan Tijjaniyya ne, kuma kakanni na sun kasance masu son zaman lafiya da tsaro."
- Salman Garba Dogo
Ƴan sanda za su ci gaba da jajircewa a Kano
Kwamishinan ƴan sandan ya tabbatarwa al’ummar Kano cewa rundunar za ta ci gaba da yin aiki ba dare ba rana don kawar da duk wata barazana ga zaman lafiyar jihar.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da sanya idanu, tare da ba hukumomin tsaro haɗin kai domin su cimma muradunsu.
Ƴan bindiga sun kai hari a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Garo da ke ƙaramar hukumar Kabo ta jihar Kano a yankin Arewa maso Yamma.
Ƴan bindigan waɗanda suka kai hari a gidan wani attajirin ɗan kasuwa, sun yi awon gaba da ɗiyarsa bayan sun karɓi N8m daga hannunsa.
Asali: Legit.ng