Gwamnatin Tarayya za Ta Dauki Matasa Aiki, An Lissafo Abubuwan da Ake Bukata

Gwamnatin Tarayya za Ta Dauki Matasa Aiki, An Lissafo Abubuwan da Ake Bukata

  • Gwamnatin Tarayya ta fara daukar ma’aikata aiki a dai-dai lokacin da matasan kasar nan ke koka wa da tsananin rashin ayyukan yi
  • Hukumar Daukar Ma’aikata ta Tarayya (FCSC), ta fitar da sanarwar cewa an fara daukar matasa aiki, tare da sanar da hanyoyin neman gurbi
  • Gwamnati ta kuma sanar da takardun da ake bukatar mai neman aikin ya mallaka, da ranar da za a rufe karbar bayanan masu neman guraben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Daukar Ma’aikata ta Tarayya (FCSC), ta sanar da fara daukar aiki a ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Hukumar ta sanar da cewa an bude guraben aiki a matakai daban-daban da ake sa ran daukar 'yan Najeriya da ke fama da rashin aikin yi za su cike.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Tinubu
Gwamnati ta fara daukar aiki Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa an sanar da guraben daukar aikin ne ta cikin wata sanarwa da shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na FCSC, Taiwo Hassan, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Hassan ya bayyana cewa matasa da su ke da cancanta za su iya neman aikin ta hanyar shafin yanar gizon hukumar.

Gwamnatin tarayya ta fara daukar matasa aiki

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa an samar da shafin yanar gizo wanda ke dauke da dukkan bayanai kan yadda za su nema aiki.

Ya kuma jaddada cewa kowanne mai nema ya kamata ya nemi gurbin aiki guda kawai domin bai wa sauran damar nema.

Yadda matasa za su nemi aikin gwamnati

Sanarwar ta bayyana cewa lokaci ya yi da duk wanda ke da sha'awar aiki da gwamnatin tarayya ya cike bayanansa a shafin da aka tanada.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce;

“Masu neman aikin su aika da aikace-aikacen su ta hanyar wannan adireshi: https://recruitment.fedcivilservice.gov.ng.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Dole ne masu nakasa su bayyana nau'in nakasar su a cikin aikace-aikacen.”

Takardun da ake bukata a aikin gwamnati

Hukumar Daukar Ma’aikata ta Tarayya (FCSC) ta jaddada cewa masu nema su ɗora wasu daga cikin takardun da za a tantance kafin daukarsu aiki.

Takardun sun hada da:

1. Takardar shaidun karatu da neman aiki

2. Takardar shaidar Digiri ko Masters

3. Takardar Digiri/HND/NCE

4. Takardar shaida ta WAEC/NECO/NABTEB

5. Takardar shaida ta Makarantar Firamare

6. Takardar kammala NYSC

7. Takardar Shaidar Haihuwa

8. Shaidar Ƙaramar Hukuma

9. Hoto na Fasfo

10. Ranar Kammala Aikace-Aikace

Sanarwar ta kara da cewa za a rufe karɓa neman daukar aikin daga nan zuwa ranar Litinin, 10 Maris, 2025.

Matasa za su samu aikin kwastam

A baya, mun ruwaito cewa Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa sama da mutane 573,000 ne suka nemi guraben aiki 3,927 da aka bude a zangon daukar ma’aikata na shekarar 2024/2025.

Kakakin hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada, ya bayyana cewa daga cikin mutanen da suka nemi aikin, fiye da 27,000 suna da takardun digiri ko HND, wanda ke nuna cewa akwai masu cancanta a dauke su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.