Minista Ya Kare Tinubu bayan Ya Shilla Kasashen Waje Sau 32, Ya Ce Sun Yi Kadan

Minista Ya Kare Tinubu bayan Ya Shilla Kasashen Waje Sau 32, Ya Ce Sun Yi Kadan

  • Ministan harkokin ƙasashen wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya fito ya kare yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake yi
  • Yusuf Tuggar ya bayyana cewa tafiyen-tafiyen da Bola Tinubu yake yi suna da amfani wajen ƙulla alaƙa mai kyau da shugabannin ƙasashen duniya
  • Ministan ya yi nuni da cewa a tafiya ɗaya kawai da Tinubu ya yi, ya jawowa ƙasar nan masu zuba jari har na dala biliyan biyu daga ƙasar Brazil

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan harkokin ƙasashen wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yi magana kan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake yi.

Ministan ya kare yawan tafiye-tafiyen da shugaba Tinubu ke yi zuwa ƙasashen waje, inda ya ce dole ne ya ƙara yawan waɗannan tafiye-tafiyen saboda amfaninsu ga ƙasa.

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

Minista ya kare yawan tafiye-tafiyen Tinubu
Yusuf Tuggar ya ce ya kamata Tinubu ya kara yawan tafiye-tafiyen da yake yi Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Yusuf Tuggar ya bayyana wannan ra’ayin ne a yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today', a ranar Lahadi.

Yusuf Tuggar ya kare yawan tafiye-tafiyen Tinubu

Ministan ya kare tafiye-tafiyen shugaban ƙasan, yana mai cewa abu ne na al’ada ga sabon shugaba ya nemi damarmaki da kuma ƙarfafa alaƙa da shugabannin duniya.

Ya kuma ƙara da cewa idan aka kwatanta da abin da ƙasar ta samu daga waɗannan tafiye-tafiyen, shugaban ƙasa yana buƙatar ƙara yawan zuwa ƙasashe daban-daban.

“Ba adalci ba ne a yi irin wannan hukunci. Sabuwar gwamnati ce domin an rantsar da shugaban ƙasa ne a shekarar 2023."
"A idon duniya, har yanzu sabon shugaban ƙasa ne. Dole ne ya yi hulɗa da takwarorinsa na ƙasashen duniya domin gina dangantaka mai ƙarfi."
"Za ku iya ganin amfanin waɗannan tafiye-tafiyen. Misali, tafiyarsa ta Brazil ta jawo zuba jarin dala biliyan biyu. Gaskiya, zan ce ba mu yi tafiye-tafiye sosai ba. Dole ne mu ƙara yawan waɗannan tafiye-tafiyen."

Kara karanta wannan

"Gidaje 3 na mallaka": Buhari ya fadi inda yake samun kudi bayan sauka daga mulki

- Yusuf Tuggar

Ministan Tinubu ya ce akwai kuɗi a Najeriya

Da aka tunatar da shi cewa Najeriya ba ta da kuɗin da za ta iya biyan irin waɗannan tafiye-tafiyen akai-akai, ministan ya musanta hakan.

“Najeriya tana da kuɗi. Ya ya tsadar tafiyar idan aka kwatanta da amfaninsa? Kuma, a zahiri, nawa ne tsadar tafiyar idan aka kwatanta da wasu abubuwan da shugaban ƙasa ya riga ya magance?"
“Nawa muka ɓatar kan tallafin fetur, wutar lantarki da sauran tallafi?"

- Yusuf Tuggar

A cikin watanni 19 da ya yi a ofis, shugaba Tinubu ya ziyarci ƙasashe 19 a cikin tafiye-tafiye 32 zuwa ƙasashen waje.

Tinubu ya shilla zuwa Tanzania

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tafiya zuwa birnin Dar es Salaam na ƙasar Tanzania da ke yankin nahiyar Afirika.

Shugaba Tinubu ya je ƙasar Tanzania ne domin halartar taron da za a yi na shugabannin Afirika kan makamashi, a tsakanin ranakun 27 zuwa 28 ga watan Janairun 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng