Sojoji 22 Sun Rasu bayan Kashe Boko Haram 70 a Wani Kazamin Fada

Sojoji 22 Sun Rasu bayan Kashe Boko Haram 70 a Wani Kazamin Fada

  • Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa sojoji 22 sun rasa rayukansu yayin wata fafatawa da 'yan Boko Haram a jihar Borno
  • Fiye da 'yan ta'adda 70 ne aka hallaka a artabun da aka yi tsakanin sojoji da mayakan Boko Haram ciki har da manyan dakarusnu
  • Kakakin rundunar tsaron Najeriya ya bayyana cewa an kashe wasu daga cikin manyan mayakan Boko Haram yayin da aka gwabza fadan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Rundunar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta yi nasarar hallaka 'yan Boko Haram fiye da 70 a wani farmaki da aka yi a jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sai dai kuma, rahotanni sun nuna cewa nasarar ta zo ne tare da asarar rayukan sojoji 22 da suka yi shahada a yayin artabun.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Janar Buba
An gwabza tsakanin sojoji da Boko Haram a Borno. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa sanarwar ta fito ne daga hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) inda kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya yi cikakken bayani kan farmakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji 22 sun rasa rayukansu a Borno

A cewar kakakin rundunar tsaro, farmakin ya faru ne a tsakanin sojoji da 'yan ta'adda a yankin da ya shahara da hare-haren Boko Haram da ISWAP.

"Mun rasa jaruman sojoji 22 yayin wannan gumurzu, amma mun samu gagarumar nasara ta hallaka mayakan 'yan ta'adda fiye da 70,"

- Manjo Janar Buba

An kashe manyan 'yan Boko Haram

Rundunar sojojin ta yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da ISWAP a fafatawar da suka yi a yankin Arewa maso Gabas.

Kakakin rundunar tsaro ya ce sun yi nasarar kakkabe wuraren da 'yan ta'addan suke buya, kuma an hallaka su da dama yayin da suka yi yunkurin kai hari ga sojoji.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

Harin ya jawo kashe wasu daga cikin manyan 'yan ta'addar Boko Haram da suke jagorantar kai hare hare a jihar Borno.

Sunayen manyan Boko Haram da aka kashe

Bayan kammala kai farmakin, rundunar tsaro ta bayyana sunayen manyan 'yan ta'addan Boko Haram da ta hallaka.

Miyagun sun hada da Talha, Mallam Umar da Abu Yazeed wanda sun kasance masu jagorantar sauran mayaka wajen kai hare hare.

Rundunar sojojin ta sha alwashin ci gaba da matsa lamba kan 'yan ta’adda har sai an kawo karshen su gaba ɗaya.

Kiran sojoji ga 'yan jarida a Najeriya

Vanguard ta wallafa cewa rundunar tsaro ta yi kira ga 'yan jarida da dukkan masu yada labarai da su guji wallafa sunayen sojojin da suka rasu yayin farmakin.

Rahotanni sun nuna cewa ba a so labarin ya riski 'yan uwansu kwatsam ba tare da bin hanyoyin da rundunar tsaro ta saba ba wajen isar da irin wannan sakon ga iyalan sojojin da suka rasu.

Kara karanta wannan

An kama motar makamai ana shirin shigo da ita Najeriya daga kasar Nijar

Ana sa ran cewa nan da kankanin lokaci rundunar tsaro za ta sanar da iyalan sojojin da suka rasu idan ta kammala tattara bayanai.

An kama 'yan fashi a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta sanar kama wasu matasa da ake zargi da fashi da makami.

Rahoton Legit ya nuna cewa an kama matasan ne yayin da suka tare hanya a tsakiyar birnin Kano suna fashi ga masu abubuwan hawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel