Rundunar Sojoji Ta Sake Taso Bello Turji a Gaba, Ta Fadi Abin Kunyar da Ya Yi
- Rundunar sojojin Najeriya ta caccaki hatsabibin shugaban ƴan bindiga Bello Turji bayan ya gudu ya bar mayaƙansa sakamakon matsin lambar da aka yi masa
- Kwamandan rundunar sojoji ta 1 da ke Gusau a jihar Zamfara, ya bayyana cewa Bello Turji matsoraci ne mai tserewa ya bar mayaƙansa
- Birgediya Janar Opurum Timothy ya bayyana cewa dakarun sojoji sun hallaka da yawa daga cikin mutanen shugaban ƴan bindigan
- Ya nuna godiyarsa ga mutanen ƙauyuka kan yadda suke ba da gudunmawa ta hanyar ba da bayanan sirri domin kawo ƙarshen ƴan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Kwamandan rundunar sojoji ta 1, da ke Gusau, jiihar Zamfara, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya yi magana kan shugaban ƴan bindiga Bello Turji.
Kwamandan rundunar sojojin ya bayyana Bello Turji a matsayin matsoraci wanda ya gudu ya bar mayaƙansa.

Kara karanta wannan
Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin

Source: Twitter
Birgediya Janar Timothy ya bayyana hakan ne a yammacin ranar Asabar bayan bikin wasannin sojoji na WASA na shekarar 2024 da aka gudanar a sansanin runduna ta 1, da ke Gusau, jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ce Bello Turji ya tsere
Kwamandan rundunar ya tabbatar da cewa yaƙar da sojoji suke yi wa ƴan bindiga zai ci gaba har sai an dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara.
“Turji matsoraci ne, kuma ya gudu ya bar sojojinsa saboda matsin lamba da muka yi masa."
"Mun hallaka da yawa daga cikin mutanensa, kuma za mu ci gaba da wannan yunkuri ta hanyar kai farmaki kai tsaye zuwa maɓoyarsu."
- Birgediya Janar Opurum Timothy
Birgediya Janar Timothy ya yabawa al’ummomin jihar saboda haɗin kansu, musamman wajen bayar da muhimmin bayanan sirri, wanda hakan ya kai ga nasarori masu tarin yawa wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar.
Ya yi kira ga sojoji da su ci gaba da jajircewa da dagewa a aikinsu, inda ya jaddada cewa jajircewa da sadaukarwa su ne mabuɗin samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Kwamandan sojoji ya yabawa mutanen Zamfara
Ya kuma bayyana cewa nasarorin da aka samu, an same su ne tare da goyon bayan al’umma, inda ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bayar da gudummawa wajen kawo ƙarshen ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka.
Birgediya Janar Timothy ya kuma bayyana cewa, an tsara sabbin dabaru da tsare-tsare don tabbatar da cewa an ci gaba da samun nasarori kan ƴan bindigan da ke addabar yankunan karkara na jihar.
Bello Turji ya shirya miƙa wuya
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan tsaron ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa ya bayyana cewa hatsabibin shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, na shan matsin lamba da ga wajen dakarun sojoji.
Babban hafsan tsaron ya bayyana cewa shugaban ƴan bindigan ya nuna alamun miƙa wuya ga jami'an tsaron Najeriya.
Janar Christopher Musa ya bayyana cewa take-taken Bello Turji sun nuna cewa yana son ajiye makamansa bayan sojoji sun rage masa ƙarfin iko.
Sai dai, babban hafsan tsaron ya nuna cewa mutane irin Bello Turji, bai kamata a ce sun ci gaba da rayuwa a duniya ba.
Asali: Legit.ng
