Hankula Sun Tashi bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Farfesan Jami'a a Gidansa

Hankula Sun Tashi bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Farfesan Jami'a a Gidansa

  • Ƴan bindiga sun yi ta'asa a jihar Delta bayan sun hallaka wani farfesa a jami'ar jihar Delta (DELSU) da ke Abraka a daren ranar Juma'a, 24 ga watan Janairu
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka farfesa Emeka Chukwuma ne a gidansa bayan ya dawo ziyarar ƙarshen mako kamar yadda ya saba
  • Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin kakakinta, SP Bright Edafe wanda ya ce an fara gudanar da bincike
  • Kakakin ƴan sandan ya nuna ana gudanar da binciken ne domin cafke masu aikata laifin domin gurfanar da su gaban kuliya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Ƴan bindiga sun kashe Farfesa Emeka Chukwuma, malami a jami’ar jihar Delta (DELSU), da ke Abraka.

Marigayin, mai shekaru 56, an ce an harbe shi ne lokacin da maharan suka kai hari gidansa da ke Umueji, a birnin Asaba, babban birnin jihar Delta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

'Yan bindiga sun kashe farfesa a Delta
'Yan bindiga sun hallaka farfesa a jami'ar jihar Delta Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Delta

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ya dawo gidansa ne don ziyarar ƙarshen mako kamar yadda ya saba lokacin da ƴan bindigan suka kashe shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta ce wata majiya ta bayyana cewa an kai wa marigayin hari ne a gidansa da ke unguwar St. Bridges a Umueji, Asaba, a daren ranar Juma’a.

"An kashe Farfesa Emeka Chukwuma a birnin Asaba a daren ranar Juma’a. Malami ne a jami’ar jihar Delta, da ke Abraka."
"Farfesa Chukwuma yakan dawo gida duk ƙarshen mako, abin takaici ne cewa ya dawo don ziyara kamar yadda ya saba, amma aka kashe shi a gidansa da ke unguwar St. Bridges, Umueji, Asaba."
"Yanzu haka, birnin Asaba babu zaman lafiya, muna cikin ruɗani kan halin da ake ciki."

- Wata majiya

Bayan aukuwar lamarin, mazauna garin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su kara daukar matakai kan ayyukan ƴan ta’adda da ke addabar mutane tare da kashe mazauna Asaba da sauran manyan birane a jihar mai arziƙin man fetur.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin ta'addanci a Kaduna, sun tafka barna

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Delta, SP Bright Edafe, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

SP Bright Edafe ya ce ƴan sanda sun fara bincike kan lamarin tare da nufin cafke waɗanda suka aikata wannan ta’asa.

"An kawo rahoton lamarin, kuma muna kan bincike tare da niyyar cafkewa da gurfanar da waɗanda suka aikata wannan laifi a gaban shari’a."

- SP Bright Edafe

Ƴan bindiga sun sace mutane a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu tsagerun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Kauru da ke jihar Kaduna a yankin Arewa maso Yamma.

Ƴan bindigan waɗanda suka riƙa yin harbi kan mai uwa da yabi sun yi awon gaba da wasu mutum zuwa cikin daji da ƙarfin tsiya.

Miyagun sun kuma hallaka wani mutum ɗaya bayan sun harbe shi tare da raunata wani daban sakamakon harbin bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel