Sarkin Musulmi Ya Jajanta Da Malamin Musulunci, Yayan Gwamna Suka Kwanta Dama

Sarkin Musulmi Ya Jajanta Da Malamin Musulunci, Yayan Gwamna Suka Kwanta Dama

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi ta’aziyya ga Musulmai da Kiristoci kan mutuwar Qamardeen Ajala da Engr. Sunday Makinde
  • Mutuwar Ajala, sanannen malami kuma mai gabatar da shirye-shiryen talbijin, ta faru tsakanin magariba da isha, yayin da Makinde ya rasu ranar Juma’a
  • Sarkin ya yaba da gudunmuwar marigayin Ajala wajen yada addini da ayyukan hajji inda ya yi masa addu'ar Allah ya yi masa rahama ya gafarta masa
  • Wannan na zuwa ne bayan sanar da rasuwar mutanen biyu a cikin awanni 24 da ya taba al'ummar Musulmi da Kiristoci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Sokoto - Sarkin Musulmi, Sa'ad Muhammad Abubabar ya tura sakon ta'azziya da aka yi rashin malamin Musulunci da yayan Gwamna Seyi Makinde.

Sultan wanda shi ne shugaban kungiyar NSCIA ya nuna alhinin mutuwar mutane biyu a cikin awanni 24 a Lagos da Oyo.

Kara karanta wannan

Watanni da aure, diyar mataimakiyar gwamna ta yi bankwana da duniya yayin naƙuda

Sarkin Musulmi ya jajanta da Malamin Musulunci ya rasu
Sarkin Musulmi ya tura sakon ta'azziya bayan rasuwar Malamin Musulunci a Lagos. Hoto: Hassan Ajinga Lateef.
Asali: Facebook

Yayan Gwamna Seyi Makinde ya kwanta dama

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin yada labaran Sultan ya fitar a jiya Asabar 25 ga watan Janairun 2025, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Allah ya yi wa Sunday Makinde, yayan Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo rasuwa da daddare, wayewar garin ranar Juma'a, 24 ga watan Janairun 2025.

Ɗaya daga cikin ƙannensa ya bayyana cewa Injiniya Sunday Makinde ya ru ba zato ba tsammani da misalin ƙarfe 3:20 na dare.

Tuni dai ƴan uwa da abokan arziki suka fara jimami da ta'aziyyar rashin yayan mai girma gwamna, wanda ya rasu ya bar ƴan uwa, 'ya'ya da jikoki.

Sarkin Musulmi ya jajanta mutuwar malamin Musulunci

Sarkin Musulmi ya yi ta’aziyya kan rasuwar malamin addini kuma mai shirye-shiryen talbijin, Amir Qamardeen Ajala.

Marigayin ya rasu tsakanin sallar magariba da isha a ranar Alhamis 23 ga watan Janairun 2025 a jihar Lagos.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga yanayi da yayan gwamna ya riga mu gidan gaskiya

Haka zalika, Sarkin ya jajanta wa Gwamna Makinde kan mutuwar dan uwansa, Engr Sunday Makinde,.

Sultan ya yi addu'a ga marigayi Sunday Makinde

Sultan daga bisani, ya jajanta wa iyalan marigayin da kuma al'ummar Oyo inda ya yi addu'ar Allah ya ba su duka juriyar rashi.

"Ka yi hakuri, domin mutuwar dan uwanka babba abu ne da ya wuce ikon kowa da kowa.
"Allah ya ba ku da dukkan 'yan uwanku, ciki har da mata da 'ya'yan marigayin, juriyar daukar wannan rashi mai girma."

- Cewar sanarwa daga Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya jagoranci ba da Zakka

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ya halarci taron shekara-shekara na Zakka da Waqafi da aka gudanar a Haɗejia.

Taron ya samu jagorancin Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III da sauran sarakuna da manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya.

An ƙaddamar da rabon Zakka a garin Lafiya a yankin Guri inda aka rarraba kayan amfanin gona da dabbobi ga mabuƙata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel