Ganduje Ya Sabunta Katafaren Masallaci, Malamai da 'Yan Siyasa Sun Hallara
- Dakta Abdullahi Umar Ganduje da tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase, sun halarci bude Masallacin Juma’a na Wase
- Aikin gyaran masallacin ya haɗa da ginin sashen mata, wanda aka gudanar karkashin gidauniyar Ganduje a bisa kulawar shugaban APC
- Jama’ar Wase sun yaba wa kokarin Abdulahi Umar Ganduje da gidauniyarsa, suna kiran da cigaba da hadin kai da samar da shugabanci nagari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Plateu - A ranar Jumu'a aka kaddamar da sabunta masallacin Juma’a na Wase da aka gyara tare da fadada shi, ciki har da gina sashen mata.
Aiki ya samu jagorancin gidauniyar Ganduje Foundation domin inganta rayuwar al’umma da bunkasa harkokin addini.

Asali: Facebook
Tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Ahmed Idris Wase ne ya wallafa yadda aka gudanar da bikin bude masallacin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron kaddamarwar ya samu halartar manyan baki ciki har da tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Shi kansa tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase ya shaida bikin bude masallacin.
Ganduje ya sabunta masallaci a Filato
Sanarwa ta fito daga mai taimakawa Ahmed Idris Wase kan harkokin watsa labarai, Faruk Tahir a ranar 25 ga watan Janairu, 2025 cewa Ganduje ya sabunta masallacin Jumu'a na garin Wase.
Tsohon gwamna Ganduje, wanda ke da hannu wajen gina masallacin tun zamanin mulkin soji na Janar Sani Abacha, ya jaddada muhimmancin ci gaban masallacin.
Shugaban APC ya yi nuni da cewa masallaci ba kawai wajen ibada ba ne, ya kasance cibiyar hadin kai da ci gaban al’umma.
Kalaman Abdullahi Umar Ganduje sun saka ya samu yabo daga mahalarta taron da suka fito daga yankuna daban daban.
Jama’ar Wase sun yabawa Ganduje
Jama’ar Wase sun nuna matuƙar farin cikinsu da wannan aiki, inda suka yaba wa gidauniyar Ganduje Foundation bisa jajircewarta wajen tallafa wa addini da al’umma.
Sun bayyana aikin da cewa wata alama ce ta hadin kai da shugabanci nagari, wanda ya kara nuna yadda jam’iyyar APC ke kula da jin dadin jama’a.
Manyan baki da suka halarci bude masallacin
A wajen taron bude masallacin, an yi wa manyan baki kyakkyawar tarba, ciki har da sanannun malaman addini daga sassan Najeriya daban daban.
Haka zalika an ruwaito cewa 'yan majalisar wakilai da sauran manyan shugabannin jam’iyyar APC sun halarci bude masallacin.
Jagoran taron, Ahmed Idris Wase, ya bayyana cewa wannan masallaci zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen inganta zaman lafiya da ci gaban jama’ar Wase.
Gidauniyar Ganduje Foundation ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da za su taimaka wa al’umma, musamman wajen inganta addini da ci gaban tattalin arziki.
Abba Kabir ya halarci Maulidi a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya halarci bikin Maulidi da aka gudanar a filin wasan Sani Abacha.
Abba Kabir Yusuf ya yaba da yadda aka yi taron lami lafiya da kuma mika godiya ta musamman ga Kalifan Tijjaniya, Muhammadu Sanusi II.
Asali: Legit.ng