Takaitaccen tarihin Masallaci na farko da aka gina a nahiyar Afrika a shekarar 620 - 630

Takaitaccen tarihin Masallaci na farko da aka gina a nahiyar Afrika a shekarar 620 - 630

- Masallacin farko da aka fara ginawa a nahiyar Afrika shine masallacin 'sahabbai'

- An gina shi ne a shekarar 620s zuwa 630s kuma yana nan a Massawa da ke Eritrea

- An gano cewa, Sahabban Annabi Muhammad ne suka gina shi

Masallacin farko da aka fara ginawa a nahiyar Afrika shine masallacin sahaba da ke Massawa a kasar Eritrea tsakanin shekarar 620 zuwa 630.

An yarda cewa sahaban Annabi Muhammad ne suka gina masallacin bayan da suka yi hijira don gujewa azabtarwar jama'ar Hejazi da ke Makka.

A wani labari na daban, garin Chefchaouen da ke kasar Morocco ne gari mafi kyawun kala a duniya.

An san garin da yawan samun masu zuwa yawon shakatawa saboda kusancinsa da Tangier da Ceuta.

Wannan yankin ga birnin ne yasa yake jawo hankalin masu ziyara.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

A gefe guda kuma, Frederick Oumar Kanoute, tsohon tauraron dan wasan kwallon kafa, ya sanar da cewa, bayan kammala shiri tsaf, an fara gina katafaren Masallaci na farko a birnin Sevilla da ke kasar Spain a cikin shekaru fiye da 700.

Kanoute, Bafaranshe dan asalin kasar Mali, ya sanar da fara gina Masallacin ne bayan ya tattara dalar Amurka miliyan daya ($1m) a gidauniyar neman taimakon da ya kafa a shafin yanar gizo.

Da ya ke sanar da hakan, Kanoute, dan wasa a kungiyar Sevilla FC, ya mika sakon godiya ga duk wadanda suka bayar da tallafi ta hanyoyi daban - daban.

"Ina godiya gareku, Allah ya bayar da lada ga duk wanda ya bayar da tallafi ko ya taimaka wajen yada neman taimakon kudin ginin wannan Masallaci," kamar yadda Kanoute ya wallafa a shafinsa na Tuwita bayan karewar wa'adin shekara guda na neman tallafin kudi.

Bayan Masallacin da za a gina, aikin zai hada da gina wata cibiyar al'adu da tarihi domin Musulman birnin Sevilla.

Aikin zai kasance irinsa na farko a tarihin birnin Sevilla a cikin fiye da shekaru 700.

Kanoute, wanda ya Musulunta tun yana da shekaru 20, ya shaidawa Aljazeera cewa ya sha wahalar neman Masallaci lokacin da ya koma kungiyar Sevilla FC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng