An Shiga Jimami bayan Tankar Mai Ta Sake Fashewa a Najeriya, Mutane 11 Sun Rasu
- An samu asarar rayuka bayan wata tankar mai ta fashe a jihar Enugu da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
- Fashewar tankar wacce ke ɗauke da man fetur ya auku ne sakamakon matsalar birki da ta samu wanda hakan ya jawo ta kife a kan titi kafin ta kama da wuta
- Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya jajantawa iyalan mutanen da hatsarin ya ritsa da su tare da alƙawarin ɗaukar matakan hana aukuwar irin hakan a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Aƙalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu yayin da wata tankar mai cike da man fetur ta fashe a kan babban titin Enugu-Onitsha a ranar Asabar.
Motar tankar dai ta samu matsalar birki, wanda ya jawo ta kife, inda man da take ɗauke da shi ya zube a kan titi kafin ta kama da wuta.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Asali: Original
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya jajantawa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Enugu ya jajanta kan hatsarin
Gwamna Peter Mbah ya bayyana cewa waɗanda suka jikkata suna samun kulawar likitoci a asibiti.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki matakan hana aukuwar irin hakan a nan gaba, ta hanyar aiwatar da dokokin hanya da gyaran sashen titin gwamnatin tarayya da ke cikin mawuyacin hali, cewar rahoton The Nation.
Haka kuma, ya umurci kwamandan hukumar FRSC na jihar, Franklin Agbakoba, da kwamishinan sufuri na jihar, Obi Ozor, su tabbatar cewa dukkan tankokin da ke dauke da kayayyakin mai masu iya fashewa suna da na’urorin hana malalar mai idan an samu hatsari.
“Wannan wani hatsari ne da binciken farko ya nuna cewa tankar ta samu matsalar birki kafin ta kife, sannan ta malalar da man fetur dake cikin tankin, wanda ya jawo gobara. Wannan masifa ce a gare mu, inda muka samu asarar rayuka."
"Amma kamar yadda na faɗa, bincike yana matakin farko. Ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro suna kan gudanar bincike. Muna so mu gano ainihin musabbabin wannan hatsarin."
"A halin yanzu, mun kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti don samun cikakkiyar kulawar likitoci."
"Ba za mu jira gwamnatin tarayya ta gyara sashen titin da ya lalace ba."
“Mu a matsayin gwamnati, za mu ɗauki matakan da suka dace domin a gyara sashen titin da ke cikin matsala nan take, don ka da mu sake fuskantar irin wannan hatsarin."
- Gwamna Peter Mbah
Da yake yi wa gwamnan bayani kan binciken farko da suka gudanar, kwamandan sashin FRSC na Enugu ya bayyana cewa malalar man fetur daga tankar ta faru ne sakamakon matsalar birkin da ta samu.
Adadin mutanen da suka mutu a Neja ya ƙaru
A wani labarin kuma, kun ji cewa an ƙara samun mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar man fetur da ta auku a jihar Neja.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa adadin mutanen da suka rasu sakamakon iftila'in ya kai mutum 98.
Asali: Legit.ng