Bayan Kisan Masu Kamun Kifi 20, Yan Ta'adda Sun Hallaka Kwamandan Sojoji da Wasu Jami'ai

Bayan Kisan Masu Kamun Kifi 20, Yan Ta'adda Sun Hallaka Kwamandan Sojoji da Wasu Jami'ai

  • Yan Boko Haram sun sake kai hari a sansanin soji na Malam-Fatori, inda suka kashe kwamandan soji, jami'ai biyu, da sauran sojoji
  • 'Yan ta'addan sun kai harin ne da motocin yaki, suna kona gine-gine da motoci, tare da jikkata sojoji da kuma batan wasu
  • Wannan harin ya biyo bayan wani farmaki a Damboa, inda aka kashe sojoji da dama, yayin da wasu suka bata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Maiduguri, Borno - Kwanaki biyu bayan kashe masu kamun kifi 20 a kauyen Gadan Gari na karamar hukumar Bama a jihar Borno, 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun kashe kwamandan soji.

Yan ta'addan sun hallaka wasu jami'ai biyu, da sauran sojoji a sansanin soji na Malam-Fatori, hedikwatar karamar hukumar Abadam a jihar.

Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka kwamandan sojoji
Yan ta'addan Boko Haram sun kashe kwamandan sojoji da wasu jami'ai da dama a Borno. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Asali: Facebook

Ana fargabar wasu sojoji sun bace a Borno

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Jaridar Thisday ta ce Bama na yankin Tsakiya ne na Borno, yayin da Malam-Fatori ke yankin Arewa, kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo fargabar bacewar wasu jami'ai da yan ta'adda suka kai wa sojoji da 'yan sa-kai hari yayin da suke kwaso gawarwakin manoma 40 da aka kashe a jihar Borno.

Ana fargabar sojoji da 'yan CJTF sun rasa jami'ai da dama yayin harin ISWAP, wasu kuma sun bata ko sun fada hannun 'yan ta'addan.

Wasu majiyoyin tsaro sun yi bayanin yadda 'yan ta'adda suka yiwa sojoji da jami'an hadin guiwar kwanton bauna a yankin Dumba.

An hallaka kwamandan sojoji a jihar Borno

A harin na baya-bayan nan, majiyoyi sun ce 'yan ta'addan sun kai hari kan Bataliya ta 149, sun kwace sansanin bayan sa'o'i masu yawa na fada, inda sojojin da suka tsira suka tsere.

Sahara Reporters ta kara da cewa, 'yan ta'addan sun yi amfani da motocin yaki da dama, sun kona gine-gine da motocin soji.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tsananta farautar Bello Turji, ana son kawo karshensa a kwanan nan

An samu gawarwaki, yayin da wasu sojoji suka ji rauni, kuma har yanzu ba a san inda wasu ke ba.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai kwamandan bataliya, jami'ai biyu, da daraktan kiwon lafiya na sansanin.

Wannan hari ya zo ne bayan 'yan ta'addan sun kai wani mummunan farmaki a sansanin soji na Damboa, inda aka kashe da dama, wasu kuma suka bata.

Wannan hari ya kuma shafi Bataliya ta 25, inda aka gano gawarwaki da dama bayan farmakin da aka kai a Sabon Gari da misalin karfe 4 na safiyar Asabar.

Yan Boko Haram sun yi arangama da sojoji

A baya, mun ba ku labarin cewa yan ta'addan Boko Haram sun kai sabon hari a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Tsagerun sun ƙona motocin jami'an tsaro tare da dasa ababen fashewa a harin da suka kai daga dajin Sambisa da ke jihar a Arewa maso Gabas.

Dakarun sojoji sun samu nasarar daƙile harin ƴan ta'addan bayan an ɗauki dogon lokaci ana musayar wuta wanda ya jikkata da dama daga dukan bangarorin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.