Tsofaffin Ciyamomi Sun Taso Gwamna a Gaba kan N183bn Na Kananan Hukumomi

Tsofaffin Ciyamomi Sun Taso Gwamna a Gaba kan N183bn Na Kananan Hukumomi

  • Tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jihar Osun sun nemi jin ba'asi kan yadda aka yi da kuɗaɗensu
  • Sun buƙaci gwamnan Osun, Ademola Adeleke da ya yi bayanin yadda ya yi da kuɗaɗen da aka turowa ƙananan hukumomin jihar
  • Tsofaffin ciyamomin sun zargi gwamnan da yi wa hukuncin Kotun Ƙoli karan tsaye kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Osun - Tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jihar Osun, sun ƙalubalanci Gwamna Ademola Adeleke.

Tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin sun ƙalubalanci gwamnan kan ya bayyana yadda gwamnatinsa ta kashe naira biliyan 183 da aka warewa ƙananan hukumomin jihar a cikin shekaru biyu.

An kalubalanci Gwamna Adeleke na Osun
Tsofaffin ciyamomi sun kalubalanci Gwamna Ademola Adeleke Hoto: @AAdeleke01
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wannan ƙalubalen ya fito ne daga tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi a ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin ciyamomi sun ƙalubalanci gwamnan Osun

Kara karanta wannan

Zargin neman cin hanci daga jami'o'i: Dan majalisa ya fadi yadda abubuwa suka kaya

Tsofaffin ciyamomin sun ƙalubalanci Gwamna Adeleke da ya bayyanawa al’umma yadda aka kashe kuɗaɗen ba tare da shugabannin ƙananan hukumomi da aka zaɓa ba, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Yayin da yake magana da manema labarai a madadin sauran tsofaffin shugabannin, Mista Owoeye Abiodun ya bayyana cewa dole ne duniya ta san irin kuɗaɗen da aka warewa ƙananan hukumomin jihar.

Ya bayyana cewa an ware maƙudan kuɗaɗe ga ƙananan hukumomin jihar a cikin shekaru biyu (Nuwamba 2022 zuwa Nuwamba 2024), amma ba a yi amfani da su yadda ya dace ba ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Adeleke.

"Gwamnatin Ademola Adeleke ta saɓawa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ta hanyar riƙewa tare da kashe kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta turowa ƙananan hukumomi 30 na jihar Osun waɗanda suka kai N183,196,629,321.19 daga Nuwamban 2022 zuwa Nuwamban 2024."
"Duk da cewa ayyukan da gwamnatin Adeleke ke yi sun ci karo da hukuncin Kotun Koli kan ikon cin gashin kan ƙananan hukumomi, musamman wajen harkar kuɗaɗe, mun damu matuƙa da rashin girmama hukuncin babbar kotun."

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

"Abin da ya dame mu ya ta’allaƙa ne kan yadda gwamnatin Ademola Adeleke ke gudanar da wannan zaluncin ba tare da shugabannin ƙananan hukumomi da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya ba."
"Babbar tambayar da ta fi ɗaure kai, ita ce ina sama da N183bn da gwamnatin Ademola Adeleke ta karɓa a madadin ƙananan hukumomi ta tafi? Me gwamnatin Adeleke ta yi da kuɗaɗen talakawa?"
"Yakamata gwamnatin tarayya da hukumominta su magance hakan ta hanyar tabbatar da cewa an yi wa mutanen jihar Osun adalci."

- Mista Owoeye Abiodun

Wane martani gwamnatin Adeleke ta yi?

A martanin da ya mayar, kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Kolapo Alimi, ya bayyana zarge-zargen da tsofaffin shugabannin suka yi a matsayin ƙarya da rashin gaskiya.

Ya yi alƙawarin zai mayar da martani kan alƙaluman da suka fitar da sauran batutuwan da suka shafi waɗannan zarge-zargen yadda ya kamata.

APC ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto zai cikawa ma'aikata alkawari, ya fadi lokacin fara biyan N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu nasara a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Ondo.

Jam'iyyar APC ta lashe zaɓen kujerun ƙananan hukumomi 16 cikin 18 na jihar a zaɓen wanda aka gudanar a ranar Asabar, 18 ga watan Janairun 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel