Basarake Ya Rusa Kwamitin Shari'ar Musulunci da Aka Kafa, Ya Kira Babban Limami

Basarake Ya Rusa Kwamitin Shari'ar Musulunci da Aka Kafa, Ya Kira Babban Limami

  • Sarkin Ado-Ekiti, Oba Adeyemo Adejugbe, ya rusa kwamitin Shari’a a Masallacin Juma’a domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka a yankin
  • Gwamnatin jihar Ekiti ta bayyana cewa tsarin dokar jihar ba ta amince da kotun Shari’a ko kwamitin sulhu na Shari’a ba
  • Babban Limamin Ado Ekiti ya tabbatar da kafa kwamitin, wanda ya ce yana duba lamuran gado, yana mai kore zarge-zargen da ake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ado-Ekiti, Ekiti - Sarkin birnin Ado-Ekiti, Oba Adeyemo Adejugbe ya rushe kwamitin Shari’a da aka kafa a babban masallacin Juma'a.

Basaraken ya bayar da umarnin ne a yau Asabar 25 ga watan Janairun 2025 bayan kafa kwamitin a masallacin Ado-Ekiti.

Basarake ya kira babban limami inda ya rusa kwamitin shari'ar Musulunci
Sarkin Ado-Ekiti ya rusa kwamitin da aka kafa a babban masallacin Juma'a na Shari'ar Musulunci. Hoto: Oba Adeyemo Adejugbe.
Asali: Facebook

Basarake ya rusa kwamitin shari'ar Musulunci a Ekiti

Sarkin ya yi wannan magana ne a lokacin taron da ya gudanar da sarakunan gargajiya, mutanen garin, da Babban Limamin Ado Ekiti, Sheik Jamiu Kewulere, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya ce fadi hakan a gaba masu ruwa da tsaki da sauran shugabannin Musulunci kan rashin jituwa da aka samu kan batun kwamitin Shari’ar.

Gwamnatin jihar Ekiti ta ce tsarin dokar jihar bai amince da kotun Shari’a ko kwamitin sulhu na Shari’a ba.

Kwamishinan Shari’a na Jihar, Dayo Apata, ya bayyana cewa kotunan jihar suna warware matsalolin aure da gado ba tare da matsala ba.

Dalilan rusa kwamitin shari'ar Musulunci a Ekiti

Sarkin ya ce ya kira taron domin tattaunawa kan batun, inda ya ji bayanin Limamin kan kafa kwamitin a masallacin don warware matsaloli.

Ya ce an kafa kwamitin ne don niyyar warware matsalolin cikin gida ba tare da shishigi daga waje ba.

Amma ya bayyana cewa yanayin kasar ba zai yarda a ci gaba da wannan tsarin ba duba da yawan al'umma da ke bin sauran addinai daban-daban.

Ya bukaci komawa yadda aka saba wurin warware matsaloli a baya ba tare da kafa wani kwamiti ba, inda ya umarci a rusa kwamitin nan take.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a Kudu kan kafa shari'ar Musulunci, an gano inda matsalar take

Bayani daga babban limamin masallacin Juma'a

Babban Limamin Ado Ekiti, Sheik Jamiu Kewulere, ya tabbatar da kafa kwamitin don duba lamuran gado.

Ya ce an warware wata matsalar aure kuma an dage sauraron wata a lokacin zaman kwamitin.

Ya musanta cewa kwamitin na da wani mummunan nufi, yana mai cewa an kafa shi ne kawai domin taimakawa al'ummar Musulmi idan ya kore zargin cewa akwai wani shiri na haddasa rikici.

Kungiya za ta buɗe kotun Shari'ar Musulunci

Kun ji cewa wata kungiyar Musulmai ta shirya kaddamar da sabuwar kotun shari’ar Musulunci a Oyo a ranar 11 ga watan Janairun 2025.

Wannan shiri ya jawo martani daga wasu da ke ganin kafa kotun zai kawo matsaloli ga walwala da 'yancin mutanen Kudu.

Wasu sun yi kira da a dakatar da bude kotun shari’ar Musuluncin saboda hadarin rabuwar kawuna a tsakanin mabiya addinai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.