Maganar N Power Ta Dawo, Tinubu Ya Umarci Sake Fasalinta, Matasa Za Su Caɓa

Maganar N Power Ta Dawo, Tinubu Ya Umarci Sake Fasalinta, Matasa Za Su Caɓa

  • Shugaba Tinubu ya juyo ta kan shirin N-Power bayan dakatar da tsarin saboda zargin badakala kan tsohuwar Minista, Betta Edu
  • Tinubu ya ba da umarnin sake fasalin shirin N-Power don ƙara inganta ayyukansa da tasirinsa ga rayuwar matasa a Najeriya
  • An ware sama da kayayyaki 100,000 da kuma N32.7bn don tallafa wa matasa da marasa galihu, musamman mata da matasa a fadin ƙasa
  • Shirin zai samar da rancen kuɗi da babu tsadar kudin ruwa N300,000-400,000 ga 'yan Najeriya don tallafa musu wajen kafa ko faɗaɗa ƙananan kasuwancinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin sake fasalin shirin N-Power don inganta ayyukan shirin tare da ƙara tasirinsa wajen taimaka wa matasa su samu abin dogaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dr. Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa shirin zai taimaka wa matasa wurin horo da damar kasuwanci kai tsaye.

Tinubu ya ba da umarnin dake fasalin shirin N-Power
Bola Tinubu ya umarci sake duba fasalin shirin N-Power inda ya ware biliyoyi. Hoto: Nentawe Yilwatda.
Asali: Facebook

Gobara ta lamushe wasu kayan Hukumar NSIPA

Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Dada Olusegun shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a shafin X a yau Asabar 25 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan gobara da ta kama a wurin adana kaya na hukumar NSIPA da ke karkashin ma'aikatar jin kai da walwala a birnin Tarayya Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gobarar ta yi sanadin lalacewar abubuwa masu amfani a ofishin ciki har da kayan masu muhimmanci.

An tabbatar da cewa gobarar ta lakume kayan horaswa da aka ware saboda matasan N-Power yayin da suke kiran a biya su kudinsu.

An ware kayayyakin biliyoyi domin shirin N-Power

Sanarwar ta ce don tabbatar da nasarar shirin, an ware sama da kayayyaki 100,000 don rabawa matasa, tare da ware N32.7bn don shirin tallafin jama’a a 2025.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki

An ƙirƙiri rukunin haɗin gwiwa da za su ba 'yan Najeriya damar samun rancen kuɗi na N300,000-400,000 da riba kaɗan don tallafa musu.

Manufar wannan tsari ita ce taimaka wa marasa galihu, musamman mata da matasa, su samu damar kafa ko faɗaɗa kananan sana'o'i don inganta rayuwarsu.

Shekarar 2025 za ta zama ta alheri ga 'yan Najeriya yayin da gwamnatin Tinubu ke aiki don cika burinta.

Shugaban ƙungiyar matasan N-Power ya zanta da Legit Hausa

Kwamred Muhammad Habib GMB ya ce tabbas Ministan jin kai da walwala ya tabbatar masa da hakan lokacin zantawarsu.

"Minista ya shaida mana yayin zantawarmu da shi, sannan suna kokari wurin ganin shugaban kasa ya bude musu asusun ajiyarsu tare da shahalewar biyan bashin N81bn da muke bi.
"Sannan ba da jimawa ba za a bude asusun sai su ci gaba da biyan basukan zuwa Fabrairun 2025."

- Kwamred Muhammad Habib GMB

Kara karanta wannan

"A bar mu da talaucinmu": Shettima ya fadi matsayarsa kan dogara da tallafin turawa

Matasan N-Power sun gaji da alkawarin karya

A baya, kun ji cewa Kungiyar matasa da suka ci gajiyar N-Power ta shirya gudanar da zanga-zanga kan basukan da suke bin Gwamnatin Tarayya na tsawon watanni akalla tara.

Matasan sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin ta ki biyansu hakkokinsu na watanni tara duk da kokarin shawo kan lamarin da ganawa da suka yi a lokuta da dama.

Shugaban kungiyar, Kwamred Muhammad Abubakar Habibu GMB shi ya bayyana haka ga jaridar Legit Hausa inda ya jero alkawuran da aka yi ta musu a baya ba tare da cika su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.