N540m: 'Yan Bindigan da Suka Sace Ma'aikatan Asibitin Katsina Sun Nemi Kudin Fansa
- Bayan kai hari tare da sace ma'aikatan lafiya a babban asibitin ƙaramar hujumar Kankara ta Katsina, ƴan bindiga sun buƙaci a ba su maƙudan kuɗin fansa
- Tsagerun ƴan bindiga sun buƙaci jimillar kuɗaɗen da suka kai Naira miliyan 540 domim sako mutanen da suka sace a yayin harin da suka kai
- Wata majiya ta bayyana cewa gwamnatin jihar na bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta kuɓutar da mutanen da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga da suka kai hari kan babban asibitin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina, sun buƙaci a ba su kuɗin fansa.
A yayin harin da ƴan bindigan suka kai a asibitin, sun harbi wani likita da kuma wani mutum ɗaya tare da sace wasu mutane ciki har da ma'aikata.

Asali: Twitter
Ƴan bindiga sun buƙaci kuɗin fansa a Katsina
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun nemi a ba su kuɗin fansa na Naira miliyan 540 don sakin wani ma’aikacin jinya da sauran mutanen da suka sace yayin harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin harin dai ƴan bindigan sun harbi wani likita mai suna Dr. Murtala Sale Dandashire, tare da sace wasu ma’aikatan asibitin.
Ɗaya daga cikin mutanen da aka sace da aka bayyana a matsayin Yusuf Muhammad Mairuwa, shi ne mataimakin daraktan ayyukan jinya kuma shugaban sashen jinya na asibitin.
Na wa ƴan bindigan suke nema?
Wata majiya mai inganci daga cikin iyalan waɗanda aka sace ta bayyana cewa ƴan bindigan sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 270 don sakin ma’aikacin jinyan.
Haka kuma, ƴan bindigan sun nemi wasu kuɗin fansa na Naira miliyan 270 don sakin sauran ma’aikatan asibitin da wasu ma’aikatan wani kamfanin taki da suka sace a kusa da asibitin yayin harin.
Idan ba a manta ba dai gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai asibitin, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron lafiyar ma’aikatan lafiya.
Wata majiya daga ɓangaren gwamnati ta bayyana cewa gwamnati tana aiki kan nemo hanyoyin ceto mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya.
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- Shugaban sojoji ya tallata shirin sulhu da 'yan bindiga a Katsina, Gwamna Radda ya yi martani
- Dakarun sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan bindiga, an soyw miyagu masu yawa
- Mutanen Katsina sun yi martani, ana tsoron gwamnati ta kinkimo sulhu da 'yan bindiga
Ganduje ya faɗi hanyar fatattakar ƴan bindiga
A wani labarin kuma,.kun ji cewa shugaban jam'iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana yadda ya hana ƴan bindiga samun wajen zama a Kano.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa ya yi amfani da sojoji wajen ganin cewa ƴan bindiga ba su zama gindin zama ba a dajin Falgore.
Ganduje ya ce dabarar da ya yi ita ce, sanyawa sojojin sun gina wajen horarwa wanda hakan ya sanya suka fattaki ƴan bindiga daga dajin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng