'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ta'addanci a Kaduna, Sun Tafka Barna

'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ta'addanci a Kaduna, Sun Tafka Barna

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane biyar a yayin harin tare da raunata wani mutum guda bayan sun kai harin a cikin dare
  • Sakataren ƙungiyar ci gaban al'ummar ƙaramar hukumar Kauru na ƙasa, Danbaba Katuka, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kuma kashe wani mutum

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƴan bindiga sun kai hari a jihar Kaduna inda suka sace aƙalla mutane biyar.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Akansan Garmadi, yankin Rumaya na ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun sace mutum biyar a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sakataren ƙungiyar ci gaban al’ummar ƙaramar hukumar Kauru na ƙasa, Danbaba Katuka, ya bayyana hakan a wata hira ta wayar tarho da jaridar The Punch a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Ƴan bindigan sun kuma kashe wani matashi mai shekaru 27, Piti Ezekiel, a wani sabon hari da suka kai ƙauyen.

Ya bayyana sunayen mutanen da aka sace da suka haɗa da Afiniki Baban Gida (46), Afiniki Timothy (41), Talatu Timothy (40), Manayi Abu (36), da Richard Dalhatu (42).

Danbaba Katuka ya bayyana cewa ƴan bindigan sun harbi wani mai riƙe da muƙamin sarautar gargajiya a masarautar Kumana mai suna Timothy Daure (48).

Sakataren ƙungiyar ya bayyana cewa ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10:30 na dare.

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kai hari daga wurare daban-daban inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Ƴan bindiga sun addabi mutanen Kauru

A cikin ƴan kwanakin nan, ƙaramar hukumar Kauru ta zama wurin da rashin tsaro ke ƙara ta’azzara, inda lamarin ya durƙusar da harkokin tattalin arziƙi, tare da tilastawa mutane da dama barin gidajensu.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

"Yawancin mazauna ƙauyukan Kauru sun bar gidajensu saboda ayyukan ƴan bindiga, inda mutane da yawa suka gudu suka bar amfanin gona a gonakinsu saboda tsoron hare-hare ko a sace su."
"Mutane sun shirya bayar da dukkanin goyon bayan da ake buƙata domin magance matsalar tsaro a ƙauyukan Kauru."

- Danbaba Katuka

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai haifar da ɗa mai ido ba.

Ba a samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba.

Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na rundunar Fansan Yamma, sun yi ruwan wuta kan ƴan bindigan da ke addabar mutane a jihar Neja.

Sojojin saman sun yi luguden bama-bamai a maɓoyar ƴan bindiga da ke a dajin Alawa cikin ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar.

Dakarun sojojin sun hallaka ƴan bindiga masu yawa a yayin harin tare da lalata wuraren da suke ajiye kayan aikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng