Kasafin 2025: An Samu Tsaiko a Shirin Komawa Aikin Majalisar Wakilan Tarayya
- Majalisar wakilai ta ƙasa ta ɗage ranar komawa hutu daga ranar 28 ga watan Janairu, 2025, ta ƙara mako guda
- A wata sanarwa da kakakin majalisar wakilan ya fitar, ya ce an sanar da kowane ɗan majalisar cewa sai ranar 4 ga watan Fabrairu, 2025 za a koma aiki
- Sanarwar ta ce an ƙara mako guda ne domin bai wa kwamitoci damar ƙarasa aikin zama da hukumomin gwamnati kan kasafin kuɗin 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar Wakilai ta Tarayya ta ɗage ranar komawa hutun majalisar da mako guda saboda ci gaba da kare kasafin kuɗin 2025.
Majalisar ta sanar da dage ranar komawa hutun daga ranar Talata, 28 ga Janairu, 2025 zuwa ranar Talata, 4 ga watan Fabarairun 2025.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar, Hon. Akintunde Rotimi ya fitar ranar Juma'a kuma aka wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar Wakilai ta kara hutu da mako guda
Rotimi ya bayyana cewa an sanar da wannan canji ga dukkan ‘yan majalisar ta hannun sakataren Majalisar, Dr. Yahaya Danzaria, bisa umarnin shugabanni.
A cewar sanarwar da aka rabawa manema labarai, Majalisar ta ce ɗage dawowa hutun ya zama dole domin bai wa kwamitoci damar kammala aikin kasafin kudin 2025.
Ta ce ƙarin zai taimakawa kwamitocin majalisa su gama aikinsu na zama da ma'aikatu da hukumomin gwamnati, waɗanda ke kare kasafin da aka ware masu.
Dailin ƙarawa ƴan Majalisa hutu
Hakan na nufin Majalisar na ƙoƙarin tabbatar da cewa an gudanar da wannan muhimmin aikin a tsanake ba tare da samun wata tangarɗa ba.
Sanarwar ta bayyana cewa:
“Ɗage dawowa daga hutun na da matukar muhimmanci domin bai wa kwamitocin isasshen lokaci su kammala aiki kan kasafin kudi da kare kasafin kowace ma'aikata."
"Wannan zai ba majalisar damar gudanar da ayyukanta cikin kwarewa da bin ka’idoji.”

Kara karanta wannan
"Ya karya doka," An tsige ɗan Majalisar APC daga kujararsa, INEC za ta canza zaɓe
Bugu da ƙari, sanarwar ta jaddada cewa wannan mataki na daga cikin dabarun majalisar wajen tabbatar da cewa ta sauke nauyin da ke kanta na duba da kuma ingancin kasafin kudin 2025.
An bayyana cewa wannan aiki yana daya daga cikin manyan nauyukan da ke gaban majalisar a halin yanzu, kuma yana bukatar cikakken lokaci da kwarewa don amfanin ƴan Najeriya baki daya.
Majalisar Wakilai ya godewa ƴan ƙasa
Majalisar ta kuma gode wa ‘yan kasa da duk masu ruwa da tsaki bisa fahimtar wannan mataki da ta ɗauka na ƙara hutun mako guda.
Har ila yau majalisar ta jaddada kudurinta na gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da adalci.
“Mun kuduri aniyar cika alkawuran mu ga ‘yan Najeriya, kuma muna godiya da fahimtar masu ruwa da tsaki,” in ji sanarwar.
Za a ci gaba da tattaunawa da kare kasafin kudi tsakanin majalisar da hukumomin gwamnati har zuwa lokacin da za a kammala kafin ranar 4 ga Fabrairu, 2025.
Majalisa ya gayyaci ministoci 2
Kun ji cewa Majalisar Wakilai ta gayyaci ministan kasafin kudi da takwaransa na ma'aikstar kuɗi kan kuɗin da aka warewa ma'aikatar ma'adanai a 2025.
Kwamitin haɗin guiwa da ke aikin tsefe kasafin kuɗin 2025 ne ya ɗauki wannan matakin bayan ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya shure gayyatar farko.
Asali: Legit.ng