Shugaba Tinubu Ya Kara Gwangwaje Gawuna da Muƙami, Ya ba Shi Kujera Mai Girma
- Tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓe 2023, Dr. Nasiru Gawuna ya sake samun mukami a gwamnatin tarayya
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Nasiru Gawuna a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na bankin Mortgage na ƙasa
- Wannan dai na zuwa ne bayan naɗin da shugaban ƙasar ya yi ws Gawuna a 2024, inda aka ba shi muƙamin shugaban gudanarwa na Jami'ar BUK ta Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake naɗa ɗan takarar gwamnan jihar Kano a inuwar APC a zaɓen 2023, Dr. Nasiru Gawuna a muƙami a gwamnatin tarayya.
Mai girma shugaban kasa ya naɗa Gawuna a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na bankin Mortgage, mai ba da lamunin gidaje a Najeriya.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X yau Juma'a.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya ba Gawuna muƙami
Kafin wannan naɗin, Gawuna, tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano shi ne shugaban majalisar gudanarwa ta Jami'ar Bayero watau BUK.
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Gawuna a wannan muƙami a Jami'ar BuK ne a shekarar 2024.
Nasiru Yusuf Gawuna ya zama mataimakin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje bayan murabus din Farfesa Hafiz Abubakar a karshen shekarar 2018.
Bayan kammala wa'adi biyu na Ganduje. ya tsayar da Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi a inuwar APC amma ya sha ƙasa a hannun NNPP.
Yadda Gawuna ya nemi zama gwamnan Kano
Guguwar jam'iyyar NNPP karkashin jagoranci tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ce ta hana Nasiru Gawuna zama magajim Ganduje.
Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya fi shahara da Abba Gida-Gida a lokacin zaɓe, shi Allah ya ɗora a kujera lamba ɗaya a Kano a zaɓen 2023.
Hakan ya sa a 2024, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Nasiru Gawuna a matsayin shugaban majalisar gudanarwa a Jami'ar BUK.
Kusan shekara guda bayan wannan naɗi, yanzu kuma Bola Tinubu ya saƙe naɗa shi a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na bankin ba da lamuni watau Mortgage Bank.
Gawuna da Ganduje sun samu sababbin muƙamai
Shugabar ƙasar ya sanar da naɗin Gawuna ne tare da wasu mutum 44 da aka naɗa a hukumomin gwamnati daban-daban.
Daga cikin waɗanda suka samu muƙami a sababbin naɗe-naɗen Tinubu har da mai gidan Gawuna kuma shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje.
Mai girma shugaba Tinubu ya naɗa Ganduje a matsayin shugaban Majalisar gudanarwa na hukumar kula da harkokin jiragen sama watau FAAN.
Tinubu ya amince a rabawa talakawa N4bn
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Tinubu ya amince a rabawa ƴan Najeriya masu ƙaramin karfi Naira biliyan 4.
Ana fatan shirin rabon tallafin zai amfani gidaje miliyan 10 da suka fi fama da matsaloli, musamman waɗanda suka rasa matsugunansu a Arewa maso Gabas
Asali: Legit.ng