Ajali Ya Yi: Gwamna Ya Yi Babban Rashi, Ɗan Uwansa Ya Rasu da Tsakar Dare

Ajali Ya Yi: Gwamna Ya Yi Babban Rashi, Ɗan Uwansa Ya Rasu da Tsakar Dare

  • Allah ya yi wa Sunday Makinde, yayan Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo rasuwa da daddare, wayewar garin yau Juma'a, 24 ga watan Janairu
  • Ɗaya daga cikin ƙannensa ya bayyana cewa Injiniya Sunday Makinde ya ru ba zato ba tsammani da misalin ƙarfe 3:20 na dare
  • Tuni dai ƴan uwa da abokan arziki suka fara jimami da ta'aziyyar rashin yayan mai girma gwamna, wanda ya rasu ya bar ƴan uwa, 'ya'ya da jikoki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya rasa dan uwansa wanda ke gaba da shi, Injiniya Sunday Makinde.

Yayan gwamnan ya rasu a safiyar ranar Juma’a, 24 ga Janairu, 2025 a gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo a Kudu maso Yammacin Najeriya.

Gwamna Seyi Makinde.
Yayan gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya rasu Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Marigayin ya rasu yana da shekaru 65 a duniya, kamar yadda aka bayyana a wata sanarwa da wani ƙaninsa, Cif Olumuyiwa Makinde, ya fitar da safiyar nan, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Watanni da aure, diyar mataimakiyar gwamna ta yi bankwana da duniya yayin naƙuda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanar da rasuwar yayan Gwamna Makinde

Cif Olumuyiwa Makinde, wanda shi ne Bada Olubadan na Ibadanland kuma shugaban gidan Aigbofa na Oja’ba a Ibadan, ya bayyana cewa rasuwar yayansu, Injiniya Sunday ta jijjiga su.

A cewarsa, wannan rashi ya jefa iyalan gidansu da sauran ƴan uwa da abokan arziki cikin juyayi da alhini.

"Cike da nauyin zuciya, ina sanar da rasuwar yayana, Injiniya Sunday Makinde, wanda ya koma ga Ubangiji a yau, Juma’a 24 ga Janairu, 2025."
"Ya rasu ne kwatsam ba zato ba tsammani a gidansa da ke Ibadan da karfe 3:20 na safiyar yau, Juma’a 24 ga Janairu, 2025."
“Ya rasu ya bar ‘yan uwa, daga cikinsu akwai gwamnan jihar Oyo, Mai girma, Engr. Seyi Makinde, yara da jikoki.”

Rasuwar ta girgiza Gwamna Makinde

Wannan labari mai cike da jimami ya girgiza ‘yan uwa da abokan arziki na marigayin, musamman ma Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Marigayin ya bar ‘yan uwa da dama, ciki har da Gwamnan Jihar Oyo, wanda ƙani ne a wurinsa, kamar yadda Channels tv ta kawo.

A matsayin dan uwa mai muhimmanci, Injiniya Sunday Makinde ya kasance ginshiki a rayuwar danginsa, tare da bayar da gudummawa ta musamman wajen kyautata alaka a cikin gida da wajen iyali.

An tura saƙon ta'aziyya ga iyalan mamacin

Yanzu haka, iyalai da abokan arziki na ci gaba da jimami da alhinin rashin wannan babban mutum mai kauna da kishin dangi.

An bayyana cewa za a sanar da shirye-shiryen jana'izar marigayin nan gaba, inda ake sa ran za a gudanar da taron addu’o’i don tunawa da rayuwarsa da irin gudummawar da ya bayar ga iyali da al’umma.

Tsohon ɗan majalisa ya rasu a Ibadan

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya yi jimami bisa rasuwar tsohon Ɗan majalisar tarayta kuma tsohon shugaban hukumar (OYSAA), Temilola Segun Adibi.

Gwamna Makinde ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan mamacin yana mai cewa ba su kaɗai wannan rashin ya shafa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel