Ganduje Ya Fadawa Sojojin Najeriya Dabara 1 ta Kawo Karshen 'Yan Ta'adda a Arewa
- Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci sojoji su inganta salon aikinsu ta hanyar mamaye dazuzzuka domin kakkabe 'yan ta'adda
- Ganduje ya tuna yadda aka fatattaki 'yan bindiga daga dajin Falgore a Kano ta hanyar amfani da dajin a matsayin sansanin soja
- A hannu daya, Gwamna Umar Bago ya fadawa gwamnatin tarayya dabarar kiyaye hadurra da kuma inganta tsaron al'ummar Neja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya jaddada bukatar daukar matakan gaggawa kan masu aikata miyagun laifuffuka da ke boyewa a dazuka.
Ganduje ya yi wannan jawabi ne yayin ziyarar ta'aziyya ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja kan gobarar tankar mai da ta kashe mutane da dama.

Asali: Twitter
Ganduje ya ba sojoji dabarar murkushe ta'addanci
Ganduje ya ce mafita kan matsalar 'yan bindiga ita ce a mamaye dazukan da 'yan ta'adda ke buya suna aikata miyagun laifuka, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya yi tsokaci kan bukatar amfani da dabarun tsaro na kai hari a maimakon kare kai domin magance matsalar tsaro a kasar.
A cewar Ganduje, sojoji za su fi saurin kawo karshen 'yan ta'adda ne idan suka nausa daji, suka tarwatsa mabuyar 'yan ta'addar da kwace ikon dazukan.
Ganduje ya tuna da dabarar dajin Falgore
Shugaban jam'iyyar ya jinjinawa kokarin Gwamna Bago wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Neja duk da girman jiharsa da yawan dazukan da ke cikinta.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Edwin Olofu ya fitar, Ganduje ya nuna damuwa kan yadda ake daukar matakai marasa sauri wajen magance 'yan bindiga.
Ganduje ya tuna yadda ya yi nasarar fatattakar 'yan bindiga daga dajin Falgore a Kano lokacin da ya nemi sojoji su maida dajin sansaninsu na horo.
Ya ce wannan dabarar ta fatattakar 'yan ta'adda daga dajin Falgore ta tabbatar da zaman lafiya a Kano har yau.
Ganduje ya jinjinawa gwamnan Neja
Ganduje ya yi addu’a tare da mika sakon ta’aziyya ga al’ummar jihar Neja kan ibtila’in gobarar tankar mai da ta yi sanadin rasa rayuka.
Ya jinjina wa Gwamna Bago bisa kokarinsa na ci gaba da tsare lafiya a jihar duk da irin kalubalen da ake fuskanta.
Ganduje ya kara da cewa:
“Mafita ga wannan matsala ita ce a mamaye dazuka. Wai me ya sa ba za mu rika kai hari ba a maimakon kare kai?”
Gwamna Bago ya roki alfarmar gwamnati
Vangaurd ta rahoto Gwamna Bago ya gode wa Ganduje da shugabannin APC bisa nuna juyayi da goyon baya ga jihar kan wannan iftila’i da ya faru da su.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta inganta muhimman ababen more rayuwa kamar gina hanyar Suleja zuwa Minna don rage hadura a jihar.
“Mun dauki matakai don wayar wa jama’a kai kan illar dibar man fetur yayin da wata tankar mai ta faru don gudun sake faruwar irin hakan."
- Gwamna Umar Bago.
Sanata Ali Ndume ya ba sojoji shawara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Ali Ndume ya ce Najeriya za ta ci nasara kan Boko Haram idan sojojin kasar suka samu karin jiragen yaki.
Ya jaddada bukatar da gwamnatin tarayya ta fi mayar da hankali kan harkokin tsaro da jin dadin al’umma yayin aiwatar da kasafin kudi.
Asali: Legit.ng