An Yi Asara: Hukumar NEMA Ta Bayyana Barnar da Gobara Ta Yi a Kasuwar Sokoto

An Yi Asara: Hukumar NEMA Ta Bayyana Barnar da Gobara Ta Yi a Kasuwar Sokoto

  • Gobarar da ta tashi a kasuwar Karar Yan Katako a jihar Sokoto ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa ga ƴan kasuwar lamarin ya ritsa da su
  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa sai da aka kwashe kwanaki biyu sannan aka samu nasarar kashe gobarar
  • NEMA ta yi bayanin cewa gobarar wacce ta tashi a daren ranar Talata, ta lalata shaguna sama da 500 da ke kasuwar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta yi bayani kan irin ɓarnar da gobara ta yi a kasuwar Karar Yan Katako a Sokoto.

Hukumar NEMA ta bayyana cewa gobarar wacce ta tashi a ranar Talata ta lalata aƙalla shaguna guda 563.

Gobara ta yi barna a Sokoto
Gobara ta lalata shaguna a kasuwar Sokoto Hoto: @nemanigeria
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar NEMA ta sanya a shafinta na X a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hukumar NEMA ta ce kan gobarar?

Hukumar NEMA ta bayyana cewa gobarar ta kwashe tsawon kwanaki biyu tana ci kafin a samu nasarar kashe ta gaba ɗaya.

Hukumar ta ce gobarar ta shafi sashen kayan gine-gine na kasuwar, kuma ta nuna cewa wannan shi ne karo na biyu da gobara ta tashi a kasuwar cikin makonni uku da suka wuce.

Shagunan da abin ya shafa galibi suna sayar da katako, kayan rufi, bututu, da sauran kayan gine-gine.

Duk da cewa ba a tantance musabbabin tashin gobarar ta ranar Talata ba, an bayyana cewa lamarin ya jawo asarar da ta zarce Naira miliyan 50.

Gobara ta yi kwana biyu tana ci a Sokoto

"Bayan namijin ƙoƙari na tsawon kwanaki biyu don kashe gobarar, hukumar kashe gobara ta jihar Sokoto ta samu nasarar shawo kan wutar."
“Wannan shi ne karo na biyu a watan Janairu na wannan shekarar da aka yi gobara a kasuwar. Karo na farko ya faru a sashen injinan niƙa a makon farko na watan Janairu, yayin da ta biyu ta shafi sashen katako da kayan gine-gine."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

"Gobarar, wacce ta fara misalin ƙarfe 3:15 na daren ranar Talata, ta lalata kusan shaguna 563 da sayar da katako, kayan rufi, ƙusoshi da bututu."

- Hukumar NEMA

Gobara ta yi ɓarna a kasuwar Sokoto

A ranar 5 ga watan Janairu, Legit Hausa ta rahoto cewa wata gobara da ta tashi da safe ta lalata shahararriyar kasuwar hatsi ta Kara a Sokoto, inda ta ƙone hatsi da dukiyoyi wanda darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Gobarar ta lalata shaguna fiye da 50, tare da shafar gidaje da dama da ke kusa da kasuwar.

Gwamnatin Sokoto za ta tallafawa ƴan kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta yi jaje ga ƴan kasuwar da ta ritsa da su a kasuwar hatsi ta Kara.

Gwamnatin ta ba da tabbacin cewa za ta tallafawa da gobarar ta ritsa da su domin su farfaɗo daga asarar miliyoyin naira da suka yi sakamakon tashin gobarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel