Malamin da Ya Je Nijar Ya ce Sojoji Sun Tsananta Tsaro, Ya Gargadi 'Yan Najeriya
- Wani malami da ya je Nijar ya yi kira ga talakawa, musamman daga Najeriya da Nijar, su zauna lafiya duk da sabanin da ke tsakanin kasashen biyu
- Ustaz Abu Uwaisat Muhammad Shitu ya ce gwamnatin Nijar ta tsaurara dokokin shige da fice, tare da buƙatar baƙi su bi ƙa’idoji kafin ziyartar ƙasar
- Haka zalika ya yi bayani kan Qur'anic Festival da kuma muhimmancin kiyaye shari’a yayin gudanar da duk wani abu da ke da alaka da addini
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Saboda sabanin siyasa da ke tsakanin Najeriya da Nijar, mutane daga ɓangarorin biyu na cigaba da tafka muhawara mai zafi a kafafen sada zumunta.
Duk da haka har yanzu lamarin bai kai ga wata babbar illa ba a rayuwa ta zahiri, a kan haka Malamai suka yi kira ga talakawa daga kasashen biyu su guji hayaniya ko rura wutar matsalar.

Source: Facebook
Wani mai wa'azi da ya je Nijar, Ustaz Abu Uwaisat Muhammad Shitu ya wallafa bidiyo a Facebook yana gargadin 'yan kasashen biyu.
Ustaz Abu Uwaisat Muhammad Shitu ya bayyana halin da ake ciki da dokokin Nijar a halin yanzu.
Ya ce har yanzu akwai mutane daga Najeriya da ke aiki a Nijar, haka kuma 'yan Nijar suna aiki a Najeriya, lamarin da ke nuna haɗin kai tsakanin jama’ar kasashen biyu.
Tsaurara dokoki a iyakokin Nijar
Abu Uwaisat ya bayyana cewa gwamnati a Nijar ta ƙara tsaurara dokoki kan shige da fice, inda ya zama dole baƙi su tabbatar da cewa suna cike dukkan sharuda kafin shiga ƙasar.
Malamin ya ce;
“Idan za ka ziyarci wani a Nijar, ya zama lallai ka tabbatar da cewa ka yi magana da mutumin da za ka ziyarta, wanda zai sanar da gwamnati cewa kana zuwa.”
Wannan matakin na nufin inganta tsaro da hana duk wani abu da ka iya tada hankalin jama’a, tsakanin baki da 'yan gari.
Dama dai malamai sun sha jan hankalin jama’a kan bin doka da oda a duk inda suke don kaucewa samun matsala da hukumomi.
Jawabi kan bikin Qur'anic Festival
A yayin zaman wa’azi da suka je Nijar, Abu Uwaisat ya ce sun ji labarin cewa za a shirya taron Qur’anic Festival, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin malamai.
Shugaban Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi jawabi kan taron a shafin Jibwis na Facebook, inda ya bayyana yadda za a yi taron.
Sai dai Abu Uwaisat ya yi kira da a kiyaye shari’ar addini yayin gudanar da irin wannan taro, musamman da aka ji ya fito daga shugaban Izala.
Abu Uwaisat ya ce;
“Kur’ani maganar Allah ce, kuma Allah ya ce zai kare shi. Karatun Kur’ani ibada ce, saboda haka ya zama wajibi a tabbatar da cewa ana bin shari’a wajen gudanar da karatunsa.”

Kara karanta wannan
Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron
Malamin ya gargadi masu haɗa karatun Kur’ani da wasu al’adu ko gargajiya, yana cewa hakan na iya jawo lahani da rashin girmama abin da ya dace.
Ya kuma bukaci a guji duk wani abu da zai saba wa ka’idar shari’a a yayin taron, yana mai ishara da cewa ya kamata malamai su nisanci bikin.
An bukaci bayani kan Qur'anic Festival
A wani rahoton, kun ji cewa taron bikin Kur'ani da ake shirin shiryawa a birnin tarayya Abuja a wata mai kamawa.
Legit ta wallafa cewa Sheikh Adam Ishaq Adam ya bukaci malamai su kawo hujjoji da suke nuna cewa ya halasta a gudanar da taron.
Asali: Legit.ng

