Gwamnatin Kebbi Ta Ayyana Ilimi Kyauta, An Fito da Tsarin Kwadaita wa Yara zuwa Makaranta

Gwamnatin Kebbi Ta Ayyana Ilimi Kyauta, An Fito da Tsarin Kwadaita wa Yara zuwa Makaranta

  • Gwamnatin Kebbi ta ƙara yawan kuɗin da ta ke kashe wa a kan ciyar da daliban makarantu da ke fadin jihar
  • Gwamna Nasir Idris da ya bayyana haka, ya kuma ce an dauki matakin karin ne domin abinci ya wadaci yan makaranta
  • Kafin yanzu, gwamnatin jihar Kebbi ta na kashe akalla Naira miliyan 200, yanzu kuma ta yi karin Naira miliyan 150

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi - Gwamnatin Jihar Kebbi ta ƙara yawan kuɗi da za a rika kashewa a kan shirin ciyar da ɗaliban makarantun sakandare da ke fadin jihar.

Gwamnan jihar, Nasir Idris ya bayyana cewa an yi karin daga Naira miliyan 200 zuwa Naira miliyan 350 domin dafa wa daliban abinci duk wata.

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Nasir
Gwamnati ta kara kudin ciyar da dalibai a Kebbi Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Facebook

AIT ta wallafa cewa Gwamnan ya ce ba haka kawai aka yi karin ba, sai dai don son cigaban ilimi a lungu da sakon da ke jihar Kebbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nasir Idris ya ce ƙarin kudin zai kuma inganta inganci da yawan abincin da ake bai wa ɗalibai domin ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da zuwa makaranta.

Gwamnatin Kebbi ta na son inganta ilimi

The Guardian ta wallafa cewa Gwamna Nasir Idris ya ce gwamnati mai ci ta bai wa harkar ilimi muhimmanci tare da tabbatar da samar da ingantaccen ilimi.

Gwamnan, wanda ya bayyana haka a yayin ziyarar godiya da ya kai ƙananan hukumomin Suru, Koko-Besse da Maiyama, ya ce gwamnati za ta tabbata ƴan jihar sun samu ilimi.

'Ilimi kyauta ne' – Gwamnan Kebbi

Gwamnan Kebbi ya ce yanzu ilimi ya zama kyauta a jihar, domin gwamnati ce ke ɗaukar nauyin rajistar jarrabawa, kudin makaranta ga dalibai.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Gwamna Nasir Idris ya kara da cewa haka kuma ana bayar da tallafin karatu ga ɗalibai na makarantun sakandare da na gaba da sakandare.

Ya ce:

"Gwamnati tana ƙarfafa neman ilimi tare da samar da tallafi domin rage wa iyaye nauyin kuɗin karatun 'ya'yansu."

Ya bayyana cewa, zuwa yanzu gwamnatinsa ta gina sababbin makarantu guda 366 tare da gyara wasu makarantu guda 1,816 a sassan jihar.

Gwamnan Kebbi ya yi maganar noma

A bangaren noma, Gwamna Nasir Idris ya yi alƙawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da takin zamani kyauta da sauran kayan aikin gona domin inganta amfanin gona. Ya ce:

"A farkon watan Fabrairu, zan ƙaddamar da aikin noman rani tare da raba injunan famfo 30,000 masu amfani da hasken rana da gas (CNG), da kuma raba takin zamani kyauta ga manoma."

Gwamna Kebbi ya ce ya cika alkawuransa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ya bayyana cewa ya cika sama da 70% na alkawurran da ya dauka yayin yakin neman zabensa na 2023.

Kara karanta wannan

'Ni kadai ke da iko': Gwamnan APC ya rikita zaman makoki, ya gargadi maciya amana

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin wakilan jam'iyyar APC waɗanda suka zaɓe shi a zaɓen fidda gwani na 2022, inda ya gode masu bisa yadda da shi da su ka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.