Ana Tsaka da Surutu kan Taron Alkur'ani, Sheikh Shariff Saleh Ya Taɓo Abubuwa 2
- Sheikh Sharif Saleh Al-Hussaini ya yi kira ga 'yan jarida da su fifita muradun ƙasa da inganta shugabanci nagari yayin isar da rahotanni ga al'umma
- Malamin ya jaddada cewa duk wani ɗan Najeriya yana da rawar da zai taka wajen tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziki
- Sheikh Saleh ya yi kira ga shugabannin addini da su ci gaba da wa'azin haɗin kai, ƙauna, da haƙuri, tare da yin addu'a don samun zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Shariff Saleh-Al-Hussaini ya buƙaci kafofin watsa labarai su maida hankali kan abubuwa biyu.
Sheikh Shariff, shugaban kwamitin fatawa na majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya roke su da su fifita muradun ƙasa da yaɗa shugabanci nagari yayin gudanar da aikinsu.

Kara karanta wannan
Malami ya faɗi jihohi 8 da ƴan bindiga ke shirin kai hari, ya ce rayuwar sarki na cikin haɗari

Asali: Facebook
Malamin ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya gudana ranar Laraba a Abuja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Shariff Saleh ya ja hankalin ƴan jarida
Shehin malamin ya jaddada muhimmancin 'yan jarida wajen tallafa wa haɗin kan ƙasa da guje wa rahotannin da ka iya haifar da rashin jituwa tsakanin kabilu daban-daban.
Sheikh Shariff Saleh-Al-Hussaini ya ce:
"'Yan jarida su ne idanu da kunnuwa na al'umma, don haka suna da alhakin ƙalubalantar shugabanni a madadin jama'a.
"Ya kamata 'yan jarida su kasance masu himma wajen tsara ajandar ƙasa da kuma bincikar shirye-shirye da manufofin gwamnati."
Malamin ya yi wa shugabanni nasiha
Haka kuma, fitaccen malamin ya yi kira ga masu rike da mukaman gwamnati da su saurari ra'ayoyi da damuwar 'yan ƙasa kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito.
Malamin ya nuna cewa Allah bai yi kuskure ba wajen haɗa kabilu daban-daban a karkashin ƙasa ɗaya mai suna Najeriya.
Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da su ba da gudummuwa wajen inganta tsaron ƙasa, ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya, da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.
Sheikh Shariff Saleh ya ƙara da cewa kowane ɗan Najeriya yana da rawar da zai taka wajen tabbatar da ƙasar ta samu ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya kuma yi kira ga 'yan ƙasa da su ƙara kusantar Ubangiji tare da yin addu'o'i don samun zaman lafiya a sassan da ke fama da rashin tsaro.
Abubuwan da ya kamata malamai su yi
Bugu da ƙari, ya jaddada buƙatar shugabannin addini da su ci gaba da wa'azin haƙuri, haɗin kai, da ƙaunar juna ba tare da la'akari da bambancin kabila ko addini ba.
Sheikh Sheriff ya kuma nuna godiyarsa ga mahukuntan Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria, bisa ba shi digirin girmamawa kwanan nan.
"Darasi mafi mahimmanci a kan ba ni digirin girmamawa da mahukuntan ABU suka yi shi ne cewa cibiyoyinmu suna gane gudunmawar shugabannin addini wajen gina ƙasa," in ji shi.
Sheikh Ishaq ya nuna shakku kan taron Alƙur'ani
A wani labarin, kum ji cewa malamai na ci gaba da bayyana mahangarsu tun bayan sanar da shirin taron mahaddatan Alƙur'ani a birnin tarayya Abuja.
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana shakkunsa kan taron, yana mai kira ga manyan malaman su fito su yi bayanin asalin irin wannan taro a addinin Musulunci.
Asali: Legit.ng