Kasuwar Sakkwato Ta Sake Kamawa da Wuta Mako 2 Bayan Mummunar Gobara
- Gobara ta barke a kasuwar katako da ke Sakkwato, kuma har yanzu jami'an kashe gobara su na kokarin shawo kanta kafin ta kara kamari
- Wannan mummunan lamari ya faru kimanin mako biyu bayan faruwar makamancin gobarar da ta lashe shaguna da dama a kasuwar
- Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Sakkwato, Bashir Muhammad, ya shaida wa Legit cewa ana kokarin shawo kan wutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Kasuwar katako ta jihar Sakkwato na ci gaba da ci da wuta ganga-ganga kimanin makonni biyu bayan wani mummunan lamari irin wannan.
Rahotonni sun tabbatar da cewa wutar ta lalata bangaren kasuwar da bai ci wuta a gobarar da ta afku makonni biyu baya ba, kuma kawo yanzu ba a san musabbabin gobarar ba.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa, masu kashe gobara, ‘yan kasuwa, da sauran al’umma suna yunkurin kashe wutar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, wutar ta riga ta lalata shaguna da kayayyaki da dama a yayin da ake shirin duba yawan asarar da aka tafka.
Wuta ta ci kasuwar Sakkwato
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Sakkwato, Bashir Muhammad, ya tabbatar wa Legit cewa har yanzu jami'ansu su na kokarin kashe wutar baki dayanta.
Ya ce ba za su iya tantance iya asarar da aka tafka ba, amma zuwa yanzu wutar ta ci kadan kadan a wani bangaren kasuwar, yayin da jama'a ke ci cikin jimami.
Bashir Muhammad ya ce;
"Mun tura jami'an nan zuwa kasuwar, har yanzu ba za mu iya tabbatar da adadin asarar da aka yi ba, ganin cewa har yanzu wutar ta na ci ganga-ganga.
Ana fatan samun saukin gobarar Sakkwato

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Sakkwato, Bashir Muhammad ya ce ana fatan jami'an hukumar SEMA za su karasa kashe wutar murus.
Ya ce jami'ansu tare da kayan aiki su na bakin kasuwar tare da daukin jama'a, yayin da mutane ke ta kawo ziyarar jaje da ganin yadda za su taimakawa jama'a.
Shugaban ya kara da cewa har yanzu ba a kai ga tantance iyaka asarar da 'yan kasuwar su ka tafka ba, amma ana sa ran an yi asarar mai tarin yawa.
Gobara ta tashi a kasuwar Sakkwato
A baya, mun ruwaito cewa jama'a sun shiga rudani bayan an samu mummunar gobara a kasuwar Kara da ke jihar Sakkwato, wacce ta lalata shaguna sama da 50 tare da jawo asarar dukiya mai yawa.
Kayayyakin da su ka kone kurnmus a kasuwar sun haɗa da kayan abinci, inda aka kiyasta cewa abubuwan da wutar ta lakume ya haura na Naira miliyan 50, wanda ya bar jama'a a cikin dimuwa.
Hukumomin bayar da agajin gaggawa a matakan jiha, SEMA da na tarayya NEMA sun ziyarci wurin domin tantance barnar da gobarar ta yi tare da tabbatar da ba da tallafi ga 'yan kasuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng