Kwana Ya Kare: Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Kuma Babban Jigon PDP Ya Rasu

Kwana Ya Kare: Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Kuma Babban Jigon PDP Ya Rasu

  • Tsohon shugaban hukumar tallace-tallace ta jihar Oyo (OYSAA) kuma jigo a PDP, Temilola Segun Adibi, ya rasu da sanyin safiyar ranar Talata
  • Gwamna Seyi Makinde ya bayyana rasuwar Adibi, tsohon ɗan Majalisar tarayya a matsayin babban rashi da ya shafi jihar Oyo baki ɗaya
  • Makinde ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin kuma ya ba iyalansa da abokan siyasa ƙarfin hali da ikon jure wannan rashi da suka yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Tsohon ɗan Majalisar Wakilan tarayya daga jihar Oyo, Hon. Temilola Segun Adibi ya riga mu gidan gaskiya.

Hon. Temi Adibi, tsohon shugaban hukumar tallace-tallace ta jihar Oyo watau OYSAA ya rasu ne da sanyin safiyar yau Talata, 21 ga watan Janairu, 2025.

Gwamna Seyi Makinde na Oyo.
Gwamna Makinde ya yi ta'aziyyar rasuwar tsohon ɗan Majalisar tarayya, Temilola Segun Adibi Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Gwamma ya kaɗu da rasuwar jigon PDP

Kara karanta wannan

Watanni da aure, diyar mataimakiyar gwamna ta yi bankwana da duniya yayin naƙuda

Gwamna Seyi Makinde, ya bayyana rasuwar Segun Adibi, babban jigo a jam’iyyar PDP a matsayin babbar rashi ga jihar Oyo baki ɗaya, kamar yadda Guardian ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makinde ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin a wata sanarwa da ya fitar bayan samun labarin rasuwar, wacce ya ce ya girgiza shi.

Ya bayyana cewa labarin rasuwar Hon. Temi Adibi ya zo masa a matsayin abin bakin ciki da takaici mara misaltuwa.

Gwamnan ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokan siyasarsa, da kuma jam’iyyar PDP a yankin Ogbomoso.

Gwamna Makinde ya miƙa sakon ta'aziyya

Seyi Makinde ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa wanda ya sadaukar da kansa wajen tabbatar da abin da ya yi imani da shi.

"Rasuwar Hon. Temi Adibi ta girgiza ni sosai. Ina mika ta’aziyyata ga iyalansa, abokan siyasa, da kuma dukkan ‘yan jam’iyyar PDP a yankin Ogbomoso.
"Hon. Adibi ya kasance ɗan siyasa mai kima da kwazo, wanda ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban siyasar yankinsa," in ji shi.

"Jihar Oyo ta yi babban rashi" - Gwamna Makinde

Gwamnan ya kara da cewa rashin Hon. Adibi ba rashi ne da ya shafi iyalansa kadai, har ma da siyasar yankin Ogbomoso da jihar Oyo baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga yanayi da yayan gwamna ya riga mu gidan gaskiya

Ya ƙara da cewa marigayin ya yi wa PDP hidima da kwarewa da sadaukarwa, musamman lokacin da ya shugabanci hukumar OYSAA, inda ya yi ayyuka masu kyau.

Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma bai wa iyalansa da abokan siyasa ƙarfin halin da za su iya jure wannan babban rashi.

Ya kara da cewa marigayin zai kasance abin tunawa saboda kyawawan ayyukan da ya bar wa jihar.

A karshe, Gwamna Makinde ya bukaci al’umma da su ci gaba da yi wa iyalan marigayin addu’a tare da nuna goyon baya a wannan lokaci mai wahala.

Wannan rashi, a cewar gwamnan, ya zama wani tunatarwa a kan mahimmancin sadaukarwa ga al’umma, wanda shi Hon. Adibi ya nuna a rayuwarsa.

Yar Majalisar Wakilai ta kwanta dama

Kun ji cewa mataimakiyar mai tsawatarwa a Majalisar Wakilan tarayya, Hon. Adewinmi Onanuga ta riga mu gidan gaskiya.

Mrigayya Onanuga, da aka fi sani da Ijaya ta shahara a siyasar Najeriya musamman matsayin 'yar siyasa mai hazaka kuma kishin ci gaban al'umma da mata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262