"Abu Ya Zo da Ƙarar Kwana": Rundunar Ƴan Sanda Ta Shiga Jimami, Ɗan Kwamishina Ya Rasu

"Abu Ya Zo da Ƙarar Kwana": Rundunar Ƴan Sanda Ta Shiga Jimami, Ɗan Kwamishina Ya Rasu

  • Ɗan kwamishinan ƴan sandan Abuja, Tunde Olatunji Disu ya mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Litinin
  • Wannan rashi ya jefa rundunar ƴan sanda cikin jimami musamman saboda a ranar CP Disu ya je ta'aziyya gidan DPO na ofishin Ushafa wanda shi ma ɗansa ya rasu
  • Kwamishinan ya yi ta'aziyya ga iyalan DPO bisa wannan rashi tare da fatan samun rahama ga wanda ya mutu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kwamishinan rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya (FCT), Abuja, Olatunji Disu, ya yi rashin ɗansa, Tunde Disu.

Allah ya yi wa ɗan kwamishinan ƴan sandan rasuwa ne a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Litinin, 20 ga watan Janairu, 2025.

Olatunji Disu.
Kwamishinan yan sandan Abuja ya yi rashi, dansa ya rasu a hatsarin mota Hoto: FCT Police
Asali: Twitter

Hatsarin ya auku ne a ranar da kwamishinan ya kai ziyarar ta’aziyya ga wani babban jami’in ‘yan sanda (DPO), wanda shi ma ya rasa ɗansa, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har kawo yanzu babu wani cikakken bayani kan musabbabun hatsarin da ya zama ajalin ɗan kwamishinan ƴan sandan Abuja.

Kwamishinan ƴan sanda ya je ta'aziyya

Amma dai an ruwaito cewa a ranar Litinin, CP Disu ya kai ziyara ta’aziyya ga CSP A.A. Sambo, jami’in ‘yan sanda mai kula da sashen Ushafa.

Allah ya yi wa ɗan CSP Sambo rasuwa kwanan nan, wanda hakan ya jefa shi da iyalansa cikin jimami, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Yayin ziyarar ta'aziyya, kwamishinan ‘yan sanda ya yi ta'aziyya da alhini ga CSP Sambo da iyalansa bisa wannan rashi da suka yi.

CP Olatunji Disu ya kuma roki Allah ya bai wa iyalai da ƴan uwa da abokan arziki haƙuri da juriyar wannan rashi.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za ta cigaba da bayar da cikakken goyon baya ga iyalan Sambo a wannan lokaci na bakin ciki.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Kwamishina Disu ya yi wa ɗan DPO addu'a

Kwamishinan ya yi addu’ar samun rahama ga wanda ya rasu, tare da fatan Allah ya ba iyalansa damar cin wannan jarrabawa.

“A madadin rundunar ‘yan sanda ta Abuja, muna yi wa wanda ya rasu addu’ar samun rahamar Allah, kuma muna yi wa iyalana fatan samun ƙarfin hali da juriya,” in ji shi.

Ɗan kwamishinan ƴan sandan Abuja ya rasu

A halin yanzu ƙoƙarin samun karin bayani daga jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, kan rasuwar dan kwamishina ya ci tura.

An kira wayar kakakin ƴan sandan a kashe kuma an tura mata sako amma har yanzu ba ta ba da amsa ba.

Rashin ɗan Kwamishinan ‘yan sandan ya kasance abin alhini ga al’umma da kuma rundunar ‘yan sandan birnin tarayya baki ɗaya.

Tsohon babban 'dan sanda ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin sufetan ƴan sandan Najeriya (AIG), Emmanuel Adebola Longe ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: Gwamnatin Kano ta saba da 'yan sanda, ta fadi shirin da ake yi

Longe shi ne ɗan sandan da ya jagoranci tarwatsa daya daga cikin manya-manyan barayin layin dogo a yankin Arewa ta Tsakiya a 2021, haka ya sa ba za manta da shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262