'Yan Majalisa Sun Gargadi Masu Kwarfato Fetur bayan Sama da Mutum 80 Sun Babbake a Neja

'Yan Majalisa Sun Gargadi Masu Kwarfato Fetur bayan Sama da Mutum 80 Sun Babbake a Neja

  • Sanatocin Arewacin Najeriya sun bayyana takaici bisa mutuwar mutane 86 hatsarin tankar fetur a jihar Neja
  • Shugaban kungiyar, Abdulaziz Musa Yar’adua, ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji tattara man fetur idan ta fadi
  • Ya bayyana cewa irin wannan iftila'i, abu ne da za a iya kare afkuwarsa idan jama'a da hukumomi sun yi aikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni dace tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ta bayyana alhininta game da rasuwar mutane 86 a gobarar tankar fetur da ta tashi a Dikko, Karamar Hukumar Gurara, Neja.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiha (SEMA) ta bayyana a ranar Litinin cewa an binne mamatan 86 yayin da wasu da dama suke kwance a asibiti suna karbar magani.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Daily Trust ta ruwaito cewa Shugaban kungiyar, Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua, ya gargadi yan kasa su guji tattara man fetur daga wuraren da tankoki suka yi hatsari.

Sanatoci na son a rika binciken tankoki

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya sun buƙaci hukumomi da su rika tabbatar da lafiyar kowace tankar mai kafin ta hau titi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce;

“Wannan mummunan al’amari ya nuna muhimmancin sanya ido sosai da kuma aiwatar da dokokin tsaro a hanyoyinmu."
“Mun kuma yi kira ga hukumomi masu ruwa da tsaki, musamman Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), su tabbatar da cewa dukkan tankokin fetur da manyan motoci sun cancanci zirga-zirga a tituna tare da bin dokoki."

Sanatoci sun gargadi yan Najeriya

Kungiyar Sanatocin ta kuma gargadi al’umma da su guji duk wani yunkuri na tattara mai daga wuraren da tankoki su ka yi hatsari domin tsare rayuka.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Kungiyar ta ce wannan hatsarin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama, abu ne da za a iya kauce masa da dukkanin jama'a sun matakan da su ka dace.

Kungiyar Sanatocin ta kuma gargadi al’umma da su guji duk wani yunkuri na tattara mai daga wuraren da tankoki suka yi hatsari.
“Rashin bin dokokin tsaro na haifar da gagarumar barna, abin da ba za a lamunta ba. Tattara mai daga wuraren hatsari na iya jawo mummunar barna da rasa rayuka.”

Tankar mai ta fadi a Neja

A baya, kun ji cewa A kalla mutane 86 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka a wani mummunan hatsarin tankar fetur a jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa tankar ta yi hatsari ne yayin da ta kwace daga hannun direbanta, inda ta fadi, ta fashe, sannan ta kama da wuta tare da kashe bayin Allah.

Kara karanta wannan

An gano abin da zai jefa 'yan Najeriya miliyan 13 a talauci a 2025, an gargadi gwamnati

Hukumar kashe gobara ta jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana yadda ta dauki matakin gaggawa don kashe wutar, tare da bayyana cewa an dauki matakin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.