Duniya ba Tabbas: Matar Tsohon Gwamna kuma Tsohuwar Sarauniyar Kyau Ta Rasu

Duniya ba Tabbas: Matar Tsohon Gwamna kuma Tsohuwar Sarauniyar Kyau Ta Rasu

  • Uwargidan tsohon gwamnan farko na jihar Delta, Olorogun Felix Ibru ta riga mu gidan gaskiya a birnin London
  • Marigayiyar mai suna Edna Ibru, ta rasu ne a ranar Laraba 15 ga watan Janairun 2025 bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Wani daga cikin iyalin Ibru, Dr. Paul Aidido Ibru, ya tabbatar da rasuwar marigayar wacce ta kasance tsohuwar sarauniyar kyau
  • Gwamna Sheriff Oborevwori ya mika sakon ta'azziyarsa ga iyalan marigayiyar inda ya yi mata addu'ar samun rahama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Asaba, Delta - An shiga alhini a jihar Delta bayan sanar da rasuwar tsohuwar sarauniyar kyau a Najeriya, Edna Ibru bayan fama da jinya.

Marigayiyar wacce mata ce ga tsohon gwamnan farko na jihar Delta, Olorogun Felix Ibru ta rasu ne a birnin London da ke kasar Burtaniya.

Kara karanta wannan

Watanni da aure, diyar mataimakiyar gwamna ta yi bankwana da duniya yayin naƙuda

Matar tsohon gwamnan Delta ta riga mu gidan gaskiya
Gwamna Sheriff Oborevwori ya jajanta da matar tsohon gwamnan jihar ta rasu. Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori.
Asali: Facebook

Gwamna Sheriff Oborevwori ya mika sakon ta'azziya

Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wakilin iyalin Ibru, Dr. Paul Aidido Ibru, ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne yayin da Gwamna Sheriff Oborevwori ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayiyar inda ya nuna alhini kan rashin da aka yi.

Gwamnan ya tura sakon ta'azziyar ta bakin sakataren yada labaransa, Festus Ahon da sanya wa hannu a yau Asabar 18 ga watan Janairun 2025.

Oborevwori ya jajanta wa iyalan Ibru da kuma al'ummar karamar hukumar Ughelli ta Arewa inda ya ba su hakuri kan babban rashin da aka yi.

Matar tsohon gwamnan Delta ta kwanta dama

A cewar Paul, tsohuwar sarauniyar kyau a Nigeria da kuma wakiliyar farko daga Najeriya a gasar ta duniya a 1964, ta rasu a birnin London bayan gajeriyar rashin lafiya.

Paul ya ce marigayiyar ta rasu ne a ranar Laraba 15 ga watan Janairun 2025 bayan ta yi fama da jinya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga yanayi da yayan gwamna ya riga mu gidan gaskiya

“Uwarmu mai raha da son mutane Mrs. Edna Ibru, ta koma ga mahaliccinta ranar Laraba 15 ga Janairun 2025."
"Kafin rasuwarta, tana da kuzari sosai, ba mu yi tsammanin za ta bar mu da wuri haka ba. Amma ba za mu iya tambayar nufin Allah a rayuwarta ba."

- Dr. Paul Aidido

Yaushe za a birne marigayiyar a Delta?

Dr. Paul Aidido Ibru ya bayyana marigayiyar a matsayin mai son mutane da zamantakewa, uwa ga kowa, mai barkwanci, mai kula da mutane inda ya ce ta kasance cike da labarai masu kayatarwa a kowane lokaci.

Paul Ibru ya kara da cewa za a sanar da shirye-shiryen jana'izarta idan aka kammala tattaunawa nan ba da jimawa ba, cewar The Guardian.

Mahaifiyar tsohon kakakin Majalisa ta rasu

Kun ji cewa mahaifiyar tsohon shugaban majalisar wakilai, Dimeji Bankole, ta yi bankwana da duniya bayan fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

'Neman gwamna ba zunubi ba ne': Kakakin Majalisa da aka tsige ya fadi dalilin taso shi a gaba

Dattijuwar mai suna Monsurat Bankole, ta rasu ne a ranar Juma’a 10 ga watan Janairun 2025 bayan shafe rayuwarta kan tafarkin addini.

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya yi alhinin rasuwar marigayiyar inda ya bayyana irin gudunmawar da ta bayar a bangaren addini.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.